Kaduna: Sarki Ya Samu Shirgegen Muƙamin Gwamnati, Gwamna Uba Sani Ya Taya Shi Murna
- Gwamnan jihaf Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa sarkin Kauru, Alhji Ya'u Shehu Usman a matsayin Amirul Hajj na bana 2025
- Uba Sani ya ce ya naɗa basaraken saboda jajircewarsa a harkar shugabanci, riƙo da gaskiya da iya mu'amala da kuma jama'a
- A matsayin Amirul Hajj, Sarkin zai jagoranci tawagar gwamnati da za ta kula da harkonin alhazan Kaduna a lokacin Hajjin 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da nadin Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj na bana 2025.
Hakan na nufin sarkin Kauru zai jagoranci maniyyatan jihar Kaduna a aikin hajjin bana na shekarar 2025 da ake shirye-shiryen yi.

Asali: Facebook
Wannan nadin ya zo ne a daidai a lokacin da gwamnatin Kaduna ta kudiri aniyar yin kyakkyawan shiri domin tafiyar da aikin hajjin bana cikin tsari, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uba Sani ya naɗa sarki a mukami
A wata sanarwa da gwamnatin Kaduna ta fitar, Uba Sani ya bayyana cewa an zabi Sarkin Kauru ne bisa cancanta.
Sanarwar ta kara da cewa an yi la’akari da jajircewar basaraken wajen yi wa al’umma hidima, tsantsar gaskiya, da kuma irin kwarewarsa a bangaren shugabanci da tafiyar da al’amuran jama’a.
Gwamnati ta ce ta yi imanin cewa irin wannan gogewa da kwarewa za su taimaka matuka wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Ayyukan Amirul Hajji a jihar Kaduna
A matsayinsa na Amirul Hajj, Sarkin Kauru zai jagoranci tawagar gwamnati da za ta kula da alhazan Kaduna a lokacin aikin Hajjin 2025.
Zai kuma yi aiki tare da kwamiti na musamman na hajji na Jihar Kaduna, hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), da sauran hukumomin da ke da alhakin shirya tafiyar Hajji.
Bugu da ƙari, Amirul Hajj shi ke da alhakin lalubo hanyoyin inganta shirye-shirye da kyautata jin daɗin alhazai, musamman ta fuskar kula da masauki, sufuri, abinci, da lafiya a cikin kasa mai tsarki.
Gwamna Uba ya taya Sarkin Kauru murna
Gwamna Uba Sani ya bayyana farin cikinsa bisa wannan sabon nadin, inda ya taya Mai Martaba Sarkin Kauru murna tare da yi masa fatan alheri.
Ya bukace shi da ya yi amfani da kwarewarsa da basirarsa wajen tabbatar da kyakkyawan kulawa da walwalar alhazan jihar Kaduna.
Gwamnan ya kuma yi fatan cewa za a gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

Asali: Facebook
Sanata Uba Sani ya roki Allah ya ba sabon Amirul Hajj ikon sauke nauyin da aka dora masa cikin nasara, rahoton Premium Times.
A ƙarshe, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin inganta shirin aikin Hajji,
Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin cewa alhazan Kaduna sun samu sauki da gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali da jin daɗi.
Kotu ta yi hukuncin kan sarautar Zazzau
A wani rahoton, kun ji cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zama a Kaduna ta yi kori ƙarar da ake neman a tsige Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
Tsohon mai zaben sarki a masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu, ne ya shigar da karar, ya na kalubalantar nadin da Nasir El-Rufai ya yi a 2020.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng