'Dan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu Ya Gamu da Fushin Matasa, an Dakawa Motar Tallafinsa Wawa
- Matasa sun farwa motar abinci da ake zargin ta ɗauko tallafin da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu zai rabawa jama'a a jihar Gimbe
- Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun dakawa motar wawa, suka kwashe kayan da suka haɗa da shinƙafa, sukari da sauransu
- Tsohon dan takarar kujerar Majalisa a Kano, Hon. Adnan Mukhtar TudunWada ya ce abin da Seyi ke yi cin mutunci ne ga 'Yan Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Gombe - Fustattun matasa sun daka wawa kan motar da ta ɗauko kayan abinci da ake zargin ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya aika jihar Gombe.
Idan ba ku manta ba Seyi Tinubu ya ziyarci jihohin Arewa da dama, inda yake buɗa baki da jama'a da shugabannin siyasa.

Asali: Facebook
Ziyarce-ziyarcen Seyi Tinubu a Arewa
A yayin wadannan ziyarce-ziyarce, yakan kaddamar da shirin bayar da tallafin abinci ga marasa galihu a lokacin Ramadan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu na yabawa da shirin, yayin da wasu ke sukarsa, suna masu cewa yankin Arewa ya cancanci samun wani tsare-tsaren ci gaba maimakon tallafin abinci kawai.
Ɗan gwamnan Bauchi ya yi magana
Shamsuddeen Bala Mohammed, ɗan gwamnan jihar Bauchi, ya soki wannan shiri na Seyi, yana mai bukatar a samar da wani shirin ci gaban matasa mai dorewa.
Ya ce:
"Dan Allah, idan ka zo Bauchi, muna bukatar ka ba matasa ayyukan yi, Keke Nafef, kudin fara kasuwanci, cibiyoyin fasaha, da horo kan kasuwancin crypto."
"Matasan Bauchi ba sa bukatar shinkafa da abinci cikin leda a lokacin Ramadan. Su ba mabarata ba ne."
Matasa sun dakawa motar abinci wawa
Duk da cewa Seyi bai kai ziyara zuwa wasu jihohin Arewacin Najeriya ba tukuna, rahotanni sun nuna cewa kayan tallafinsa sun isa Jihar Gombe.
A wani bidiyo da wata jarida ta wallafa, an ga wasu matasa suna kwasar kwalayen kayan abinci daga wata mota da aka ajiye a gefen hanya.

Kara karanta wannan
Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027
An hango matasan sun shiga cikin motar, suna jefo kayan abincin da suka haɗa da shinkafa, sukari, man girki, gishiri, da taliya ga jama’a da ke kasa, su kuma su tsere da su.
Rahotanni sun ce an tura tireloli guda biyu dauke da kwalaye 3,500 na kayan abinci zuwa Gombe.
Ɗaya daga cikin motocin an raba kayan lafiya, yayin da ta biyun kuma ta gamu da fushin matasa, waɗanda suka wawashe kayan ciki gaba ɗaya.
Duk da cewa Seyi ya bayyana wannan shiri nasa a matsayin "Rangadin Ramadan" da shirin jawo matasa a jiki wasu masu fashin baki na ganin hakan a matsayin wata dabara ta siyasa.

Asali: Twitter
Seyi Tinubu na cin mutuncin Arewa
A wata hira da Legit Hausa ta wayar tarho, tsohon ɗan takarar Majalisar Dokokin Kano, Hon. Adnan Muktar TudunWada, ya soki ziyarce-ziyarcen Seyi Tinubu a Arewa.
A cewarsa, Arewa ta fi bukatar a bunƙasa harkokin ilimi, samar da cibiyoyin fasahar zamani, ƙarin jami'o'i da sauran ayyukam ci gaba fiye da rabon abinci.
A kalamansa ya ce:
"Ba abinci matasan Arewa ke buƙata ba, muna bukatar inganta ilimi, samar da cibiyoyin fasaha, karin makarantu da sauran ababen more rayuwa.
"Abin da Seyi ke yi a fadar sarakunan Arewa cin mutunci ne, bai isa ya yi haka a idan ya je wurin sarakunan yarbawa ba."
Bola Tinubu ya ba ƴan APC buhunan shinkafa
A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya aika gudunmawar buhunan shinkafa 7,000 a matsayin tallafin Ramadan ga ƴaƴan jam’iyyar APC a jihar Zamfara.
Ƙaramin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya kaddamar da rabon tallafin a ranar Juma’a da ta gabata.
Asali: Legit.ng