Hawan Sallah: Sanusi II Ya Dauki Zafi, Ya Yi Addu'o'i kan Masu Son Tada Tarzoma a Kano

Hawan Sallah: Sanusi II Ya Dauki Zafi, Ya Yi Addu'o'i kan Masu Son Tada Tarzoma a Kano

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya buƙaci al'ummar jihar Kano da su kwantar da hankulansu ka da su tayar da tarzoma
  • Sanusi II ya yi addu'o'i kan masu don tayar da fitina a jihar, inda ya roƙi Allah maɗaukakin Sarki da ya mayar musu da aniyarsu
  • Ya buƙaci al'ummar Kano da ka da su tankawa duk wanda ya takale su da faɗa, domin jan faɗa halayyar mutanen da aka yi nasara a kansu ne

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya kwararo addu'o'i yayin da aka fara zaman ɗar-ɗar kan hawan Sallah da za a gudanar a jihar.

Mutanen Kano dai sun shiga cikin halin rashin tabbas yayin da sarakunan guda biyu masu rigima kan sarautar Kano, suka shirya gudanar da Hawan Sallah a cikin birnin Dabo.

Kara karanta wannan

Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027

Sanusi II ya yi addu'o'i
Sanusi II ya yi addu'o'in samun zaman lafiya a Kano Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Sarkin na 16 ya yi adduo'in samun zaman lafiya a wani bidiyo da masarautar Kano ta sanya a shafinta na X a ranar Litinin, 24 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Sanusi II ya kwararo addu'o'i

A cikin bidiyon, mai martaba sarkin ya yi addu'o'in samun zaman lafiya a jihar wacce ta yi fice wajen harkokin kasuwanci.

Sanusi II ya kuma yi addu'ar Allah Ya sanya masu son tayar da rigima a Kano, aniyarsu ta mugunta ta koma kansu.

Sarkin na Kano na 16 ya buƙaci al'umma su zage damtse su ci gaba da yin addu'o'i musamman a watan Ramadan domin samun zaman lafiya.

"Duk wanda yake neman ya hura wuta a Kano, Allah ya sa wutar ta ƙone shi, duk wanda yake son hankalin mutanen Kano ya tashi, shi ma Allah ya tayar da hankalinsa."
"Allah ya tsare mana ƙasar mu, Allah ya tsare mana rayukanmu, Allah ya ci gaba da tsare mana mutuncinmu."

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Aminu Ado ya yi rangadi a Kano, ya duba filin hawan sallah

"A ci gaba da zama lafiya, a ci gaba da addu'a, kuma a irin wannan lokaci, mutane idan aka yi nasara a kansu, za su nemi su tayar da fitina, ka da a tanka musu, ka da a yarda a shiga hanya ta tashin hankali."
"Insha Allahu duk wanda yake jayayya da hukuncin Allah ba zai je ko ina ba. Allah ya ba mu zaman lafiya, Allah ya kare mana mutuncinmu da addininmu."

- Muhammadu Sanusi II

Akwai yiwuwar hana Sarki Sanusi II hawan Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ƙwararren lauya, Chidi Odinkalu, ya nuna damuwa kan yiwuwar a hana Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II gudanar da hawan Sallah ƙarama.

Ƙwararren lauyan ya bayyana cewa bayanan da suka iso gare shi, sun nuna cewa kotun ɗaukaka ƙara na shirin ba da umarnin hana Sanusi II gudanar da hawan Sallah.

A cewar Farfesa Odinkalu, wannan umarnin zai ba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, damar gudanar da hawan Sallah ƙarama a birnin Dabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng