Jami'an Tsaro Sun Gwabza da 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Aka Sace

Jami'an Tsaro Sun Gwabza da 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Aka Sace

  • Jami'an tsaro a Katsina sun yi artabu da ƴan bindiga bayan sun kai hare-hare kan bayin Allah da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Ƴan bindigan sun kai wani hari a ƙaramar hukumar Kankara, inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san yawansu ba zuwa yanzu
  • Jami'an tsaron sun yi gaggawar ritsa ƴan bindigan kafin su tsere, suka samu nasarar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile hare-haren ƴan bindiga a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar kuɓutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su a bayan sun gwabza faɗa da ƴan bindigan.

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga a Katsina
Jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga a Katsina Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Katsina

Majiyoyi sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 5:30 na asuba a ranar 23 ga Maris, 2025, ƴan bindiga sun afkawa ƙauyen Kutungubus da ke ƙaramar hukumar Kankara, suka sace wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba.

Cikin gaggawa dakarun haɗin gwiwa da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda da ƴan sa-kai suka toshe hanyar da ƴan bindigan za su tsere ta Mararraba Gurbi.

Lamarin ya jawo an yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da ƴan bindigan wanda hakan ya tilasta musu janyewa.

Bayan artabun, jami’an tsaron sun samu nasarar ceto mutum biyar, Lamunde Musa, Nafisa Isa, Umma Tanimu, Hauwau Sani da Halisa Sani.

Sai dai ƴan bindigan sun tsere da mutum uku da suka haɗa da Ayuba Ibrahim, Fariza Harisu da Guje Salihu.

Hakazalika, da misalin ƙarfe 10:30 na dare a wannan rana, wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Dungum Sambo da ke ƙaramar hukumar Dandume.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, sun yi awon gaba da babbar soja da wasu mutane

Jami’an tsaro sun yi gaggawar isa ƙauyen, inda suka yi arangama da ƴan bindigan.

A sakamakon ɗauki ba daɗin da aka yi, ƴan bindigan sun tsere cikin daji ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Ƴan sanda sun fatattaki ƴan bindiga

A wani harin na daban, da misalin ƙarfe 11:43 na dare, ƴan bindiga sun tare hanyar Sabuwa-Kaya kusa da Kwana Uku, inda suka kai farmaki kan matafiya.

Bayan samun rahoto kan lamarin, ƴan sanda sun yi gaggawar garzayawa zuwa wurin.

Da ganin jami’an tsaro, sai ƴan bindigan suka bude wuta, inda suka harbi wani matashi mai shekaru 27 mai suna Bello daga ƙauyen Layin Dan Auta da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kafin su tsere.

An garzaya da mutumin da aka harba zuwa asibitin Haske Private Hospital da ke Sabuwa domin samun kulawa.

Ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun sace wasu ɗalibai na jami'ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA).

Ƴan bindigan sun kutsa inda ɗaliban suke kwana ne a kan hanyar Tsaskiya cikin garin Dutsinma kafin su yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel