Hankula Sun Tashi bayan Bam Ya Fashe Ana cikin Azumi a Yobe
- An shiga jimami a jihar Yobe bayan wani bam da aka binnne a cikin daji ya tashi, ya ritsa da wasu mutane da ke kusa da wajen
- Lamarin fashewar bam ɗin ya auku ne a wani ƙauyen Buni Yadi, hedkwatar ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe
- Bam ɗin ya fashe ne bayan da wani matashi ya yi kaciɓus da alburusai a cikin daji sannan sai ya yi ƙoƙarin buɗe su
- Fashewar bam ɗin ya yi sanadiyyar jikkata mutane uku yayin da aka garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
JIhar Yobe - Aƙalla mutane uku sun samu raunuka kuma an kai su asibiti bayan fashewar wani bam a jihar Yobe.
Lamarin fashewar bam ɗin wanda aka binne ya auku ne a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa fashewar ta faru ne a ranar Asabar a ƙauyen Ngomari da ke garin Buni Yadi, hedkwatar ƙaramar hukumar Gujba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda bam ya fashe a Kauyen Yobe
Wata majiya mai tushe a yankin ta bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wani matashi mai shekaru 22 ya gano alburusai da kuma harsasai guda huɗu na bindigar AK47 yayin da yake nemo itacen girki a daji.
Matashin ya yi ƙoƙarin buɗe alburusan domin ganewa idonsa abubuwan da ke ciki.
"Ya ci gaba da dukan su da guduma, wanda hakan ya haddasa fashewar. Mutane uku, ciki har da matashin, sun samu raunuka daban-daban."
- Wata majiya
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, sakataren ƙungiyar ƴan bola-bola ta ƙaramar hukumar Gujba, Malam Isyaku Dahiru, ya bayyana cewa an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na jihar Yobe da ke Buni Yadi domin samun kulawa cikin gaggawa.
Ba a ji ta bakin ƴan sanda ba
Ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya ci tura.
Kakakin ƴan sandan bai ɗaga kiran da aka yi masa a waya ba har zuwa lokacin da ake kammala haɗa wannan rahoton, kuma bai biyo ba.
Ƴan ta’addan Boko Haram sun daɗe suna amfani da bama-bamai wajen kai hare-hare a yankin.
Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Yobe
A baya rahoto ya zo cewa wasu ƴan ta'adda ɗauke da makamai da ake zargin na Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a jihar Yobe da ke Arewacin Najeriya.
Ƴan ta'addan sun kai harin ne a garin Gujba inda suka kashe wani jami'in ƴan sa-kai mai shekara 22 har lahira.
A yayin harin kuma, ƴan ta'addan sun ƙona shaguna takwas tare da lalata ɗakuna 12 bayan sun riƙa bi gida-gida suna farmakar jama'a.
Ƴan ta'addan sun kuma riƙa neman ƴan sa-kai domin su hallaka su a harin wanda suka kai a cikin tsakar dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng