Basarake Ya Nemi Taimako bayan Barazanar Kisa da Wasu Matasa Ke Yi Masa

Basarake Ya Nemi Taimako bayan Barazanar Kisa da Wasu Matasa Ke Yi Masa

  • Wani babban basarake a Ilawe-Ekiti, Ajibade Olubunmi, ya ce an yi masa barazanar kisa yayin wata ganawar danginsu a ranar 15 ga Maris
  • Dattijon ya rubuta korafi ga Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ekiti, yana rokon a kare rayuwarsa daga wasu mazauna unguwar Irorin da ke masa barazana
  • Ya bayyana cewa wasu gungun mutane dauke da makamai sun kawo tsaiko a ganawar suka nemi harbinsa, amma mutane suka ceto shi kafin 'yan sanda su iso
  • Basaraken ya ce har yanzu ba a kama wadanda ake zargi ba, kuma suna yawo suna shelar cewa ba za a iya yi musu komai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ado-Ekiti, Ekiti - Wani mai sarauta a jihar Ekiti ya yi korafi ga rundunar yan sanda kan yi masa barazanar kisa.

Kara karanta wannan

Ramadan 2025: Ana tafka tsananin zafin rana a Kano, masu azumi sun koma shan ORS

Dattijon a unguwar Irorin a Ilawe-Ekiti, Ajibade Olubunmi, ya bayyana cewa wasu mutane a garin sun yi masa barazanar kashe shi.

Wasu matasa sun yi barazanar hallaka basarake
Basarake ya kai korafi ga ƴan sanda bayan yi masa barazanar kisa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda matasa ke neman hallaka basarake

A wata wasika da ya aikewa kwamishinan 'yan sanda na jihar Ekiti, Joseph Eribo, Olubunmi ya ce an nemi kashe shi a ganawa ranar 15 Maris, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa mutanen sun zo da muggan makamai wurin wata ganawa domin kai masa hari, amma mutanen gari suka ceto shi kafin isowar 'yan sanda.

Dattijon wanda kuma shi ne mai ba Oba Ajibade Alabi shawara kan kafafen yada labarai, ya bukaci a ceci ransa, yana cewa ba a kama masu laifin ba.

Wasikar na cewa:

"Ranar Asabar 15 ga Maris, 2025, ina jagorantar taron danginmu a dakin taro na Owa Oruku lokacin da wasu uku suka shigo cikin hanzari.
"Suka fara yi min barazana, suna nuna bulala, suna zagi, daya kuma yana kokarin fidda bindiga domin harbe ni, da na tashi, sai naga wasu sun kewaye dakin."

Kara karanta wannan

'Wani gwamnan Najeriya zai mutu kafin 2027': Malami ya hango makomar Atiku, Tinubu

Yadda matasa suka yi barazanar hallaka basarake a Ekiti
Basarake ya yi korafi ga yan sanda bayan yi masa barazanar kisa. Hoto: Oyebanji.
Asali: Facebook

Rokon da basaraken ya yi ga al'umma

Basaraken ya bayyana yadda mutane suka ceto rayuwarsa daga miyagun da suka yi kokarin hallaka shi.

"Tsoma bakin wasu daga cikin 'yan uwa ne ya hana a harbe ni, an kira ‘yan sanda, sai suka zo amma maharan uku suka tsere da sauran mutanen nasu."
"Har yanzu ba a kama su ba, kuma wanda ya tabbatarwa ‘yan sanda zai kawo su bai cika alkawari ba."
"Kwamishinan ‘yan sanda, na san sunan wadanda suka shigo dakin, dukkansu mazauna Irorin ne kuma ‘yan sandan Ilawe sun gan su."

Dattijon ya roki al'umma su ceci rayuwarsa domin wadannan mutane suna yawo cikin gari ba tare da an kama su ba, suna cewa ba za a iya musu komai ba.

Gwamna ya yi zama da sarakuna kan rikici

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Osun ya sake kakabawa garuruwan Ifon da Ilobu dokar hana fita daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

Kara karanta wannan

Bayan sace ɗaliban jami'a, ƴan bindiga sun sake komawa Katsina, sun kashe mutane

Ademola Adeleke ya umarci sarakunan Olufon da na Olobu da sauran masu ruwa da tsaki su halarci taron yin sulhu.

Rikici ya sake barkewa tsakanin al’ummomin biyu, inda wani tsohon kansila daga Ifon, mai suna Azeez, ya rasa ransa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng