Kaduna: 'Yan Daba Sun Kutsa cikin Masallaci, Sun Yi Kisan Kai Ana Sallar Tarawi

Kaduna: 'Yan Daba Sun Kutsa cikin Masallaci, Sun Yi Kisan Kai Ana Sallar Tarawi

  • ‘Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargi da kai hari a masallacin Layin Bilya, Rigasa, yayin sallar Tarawihi, inda suka kashe matashi
  • Maharan sun daba wa Usman Mohammad wuka, in da aka garzaya da shi asibiti, amma daga baya ya rasu sakamakon raunukan da ya samu
  • Sai dai, mazauna layin Magaji da ke kusa da layin da abin ya faru, sun koka kan cewa an hada da wani mai faci a cikin wadanda aka kama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama mutum 12 da ake zargi da kai hari kan masu ibada a Rigasa, karamar hukumar Igabi.

Harin ya faru ne yayin sallar Tarawi a Layin Bilya, kan titin Makwa, Rigasa, inda wasu ‘yan daba dauke da makamai suka far wa wani matashi dan-sa-kai.

Kara karanta wannan

Bayan sace ɗaliban jami'a, ƴan bindiga sun sake komawa Katsina, sun kashe mutane

'Yan sanda sun magantu da 'yan daba suka kashe matashi a cikin masallacin Kaduna
'Yan daba sun kashe matashi dan sa kai ana tsaka da sallar Tarawi a jihar Kaduna.
Asali: Getty Images

'Yan daba sun kashe matashi a cikin masallaci

Mai magana da yawun ‘yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maharan sun daba wa matashin mai suna Usman Mohammad, mai shekara 23, wuka, inda aka garzaya da shi asibiti amma daga bisani ya rasu.

Mansir ya ce ‘yan daban sun fito ne daga unguwannin Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza da Unguwar Badiko kafin kai harin da misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Ya bayyana cewa bayan samun labarin harin, DPO tare da tawagar ‘yan sanda da kuma rundunar CJTF sun dira wurin domin kama masu laifin.

An cafke mutane 12 kan zargin kashe matashin

A cewarsa, an cafke mutum 12 da suka amsa cewa suna cikin wadanda suka kai harin, kuma an kwato makamai daga hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Rundunar ‘yan sanda ta dauki matakan tsaurara tsaro a masallatai da sauran wuraren ibada don hana sake aukuwar irin wannan hari a gaba.

Hassan ya bukaci al’ummar yankin da su kasance masu sa ido tare da gaggauta sanar da hukuma idan sun ga wani abu da ba su yarda da shi ba.

Ya kuma gargadi masu aikata irin wadannan laifuka da su daina, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.

An kama mai faci bayan harin masallaci

Mazauna layin Magaji sun koka kan yadda aka kama wani mai faci a daren da aka farmaki masallacin Kaduna
Kaduna: Mazauna layin Magaji, sun roki 'yan sanda su duba batun wani mai faci da aka kama a cikin wadanda ake zargi. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wakilin Legit.ng Hausa da ya ziyarci Makarfi Road, kan titin da aka yi aika-aikar, ya zanta da wasu mazauna layin Magaji, inda suka koka kan kama wani mai faci a daren da aka yi kisan.

Mazauna wannan unguwa, sun shaida cewa mai facin, mai suna Muhammadu, ya kasance dan-sintiri ne, kuma ya fita aiki a daren da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Majiya daga unguwar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa wakilinmu cewa:

"A iya saninmu, Muhammadu yana daga cikin 'yan sintiri da ke ba layin Magaji da Tijjani Baba kariya, kuma muna da yakinin ya fita aiki a daren da aka yi kisa a layin Mokwa.
"Muna cikin Sallar Tarawi, wani matashi ya shigo masallaci da gudu, ya ce mu rufe kofofi, unguwar ba lafiya. Bayan karfe 2:00 na dare, muka fita, shi ne muka ji abin da ya faru.
"A cikin wadanda aka kama, akwai Muhammadu, wanda a nan layin na Magaji ya ke yin faci, da gadin na'urorin MTN da ke cikin layin, ba mu san shi da ta'addanci ba."

Majiyar ta ce tuni suka tuntubi lauya domin ganin Muhammadu ya samu mafita daga wannan zargi, musamman ganin cewa ya samu karaya a kafarsa.

"Da aka samu damar ganin Muhammadu, an tabbatar akwai karaya a kafarsa, sai 'yan sanda suka ba da damar dora shi. Yanzu haka muna kokarin ganin ya samu adalci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta raba tallafin kudin noma ga mutane 250,000

"Muna fatan binciken 'yan sanda zai wanke wannan bawan Allah, domin kowa ya yi masa shaidar arziki, ba shi da abokin fada, kullum yana wajen sana'arsa.
"Yanzu haka a masallacinmu ne muke nemawa iyalinsa taimako saboda su samu damar yin sahur da buda baki, tun da shi mai nemowa, sannan mun hada kudin dora shi."

'Yan unguwar Magaji, sun roki 'yan sanda da za su duba lamarin Muhammadu, suna masu jaddada cewa, an samu kuskuren fahimta ne a lokacin da aka kama shi.

'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun halaka shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na karamar hukumar Barkin Ladi, Jihar Filato.

Rahotanni sun ce maharan sun kai farmaki gidansa a daren Laraba, 19 ga Maris, 2025, inda suka kashe Muhammad Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel