Bayan Jita Jita, Fubara Ya Bayyana a Bainar Jama'a da Ya Kawo Karshen Rade Radi
- Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana a bainar jama'a karo na farko bayan dakatarwarsa daga ofis, ya je coci a yau Lahadi
- Fubara ya halarci taron ibada a Port Harcourt, inda wani babban fasto ya tarbe shi tare da raka shi cikin coci
- Bayyanar Fubara ta kawo karshen jita-jitar da ke yawo kan inda yake tun bayan dakatarwar da aka masa
- Dakataccen gwamnan ya iso da kananan motocin tawaga ba tare da tutar gwamnati ko tambarin ofishin gwamna ba wanda ya je tabbatar da rasa ikonsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana a bainar jama'a karo na farko a yau Lahadi bayan dakatar da shi.
Kafin wannan lokaci, an fara yada jita-jita kan halin da yake ciki tun bayan karbe iko daga hannunsa a Rivers.

Kara karanta wannan
An fadi halin da Fubara ke ciki bayan shugaban rikon kwarya ya shiga ofis a Rivers

Asali: Twitter
Rivers: An fadi halin da Fubara ke ciki
An tarbe shi daga wani babban fasto wanda ya raka shi cikin cocin ne domin ya shiga cikin taron ibada da ake gudanarwa, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin Simi Fubara da aka dakatar, Nelson Chukwudi, ya tabbatar da gwamnan ya na lafiya kuma babu matsala da lafiyarsa.
Chukwudi ya bayyana hakan ne a wata hira da yan jaridu yana mai karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Hadimin ya ce mutane su yi watsi da labaran da suke gani a shafukan intanet domin babu barazanae da ke fuskantar Gwamna Fubara.
Duk da rikicin siyasa, Fubara yana cikin kwanciyar hankali kuma yana ci gaba da gudanar da rayuwarsa cikin koshin lafiya.

Asali: Instagram
A gano Fubara karon farko bayan rasa kujerarsa
An hangi Fubara a cocin 'Salvation Ministry' dake Port Harcourt, inda yake bautawa, lamarin da ya kawo karshen rade-radin da ake yi.
Gwamnan ya iso wurin da 'yan tawaga kadan ba tare da tutar gwamnati ko tambarin ofishin gwamnan ba.
Majiyoyi suka ce wannan bayyana ta Fubara ta kawo karshen jita-jitar cewa dakataccen gwamnan na cikin wani irin hali.
Dakatar da Fubara ya jawo ka-ce-na-ce musamman daga jam'iyyun adawa da ke ganin akwai siyasa a matakin da Bola Tinubu ya dauka a Rivers na sanya dokar ta-ɓaci.
Wasu kuma sun yi zargin hakan bai rasa nasaba da neman karbe ikon jihar saboda zaben 2027 duba da yadda jihar ke da matukar tasiri a siyasar Najeriya tun tali-tali.
Rivers: SERAP ta maka Tinubu a kotu
A wani labarin mai kama da wannan, mun ba ku labarin cewa Ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Kungiyar SERAP ta maka Shugaba Tinubu ƙara a gaban kotu inda take ƙalubalantar matakin da shugaban ya ɗauka wanda ya jawo magana a kasa baki daya.
Rahotanni sun ce ƙungiyar.ta buƙaci kotun da ta soke dakatarwar da aka yi wa zaɓaɓɓun shugabanni domin a cewarta hakan ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng