Wata Sabuwa: Zanga Zanga Ta Barke kan Takaddamar Sanata Natasha, an Samu Bayanai

Wata Sabuwa: Zanga Zanga Ta Barke kan Takaddamar Sanata Natasha, an Samu Bayanai

  • Masu goyon bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025
  • Mutanen na Kogi ta Tsakiya sun fito kan tituna ne domin nuna adawa da shirin da wasu ke yi na yi wa Sanata Natasha kiranye daga majalisar dattawa
  • Sun nuna cewa ƙoƙarin raba Sanata Natasha da kujerarta mayunwata ne waɗanda aka ba su kuɗi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Ɗaruruwan mutanen Kogi ta Tsakiya sun fito zanga-zangar nuna goyon baya ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Mutanen dai sun fito kan tituna ne domin nuna goyon baya ga Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce ke wakiltar yankin a majalisar dattawa.

Zanga zanga ta barke saboda Natasha
Magoya bayan Sanata Natasha.sun gudanar da zanga-zanga Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta rahoto cewa an gudanar da zanga-zangar ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta dakatar da Natasha

Majalisar dattawa dai ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga watan Maris bisa zargin rashin ɗa'a bayan da ta samu saɓani da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a majalisar.

Kara karanta wannan

Kotu ta ceto Sanata Natasha daga barazanar raba ta da kujerarta

Tun da farko, ta zargi Akpabio da cin zarafinta ta hanyar yunƙurin yin lalata da ita.

Masu zanga-zanga sun fito saboda Natasha

Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da wasu mutanen mazaɓar Kogi ta Tsakiya suka fara ƙoƙarin gudanar da shirin raba Natasha Akpoti-Uduaghan daga muƙaminta.

Masu zanga-zangar sun ɗauki alluna masu ɗauke da saƙonnin da ke cewa: "Natasha, alfaharin Kogi ta Tsakiya", "A kare mutanen mazaɓar Kogi ta Tsakiya", da "Muna tare da Natasha".

A cikin masu zanga-zangar, akwai maza, mata, da matasa, inda suka riƙa rera waƙoƙi a harshen Ebira, suna yi wa wadanda suka fara shirin yi wa Sanata Natasha kiranye ba’a.

Tare da haɗa baki, sun riƙa rera waƙa suna cewa:

"Ya kamata su ji kunya! Kunya ta kama su bayan sun karɓi Naira 10,000 da jollof rice daga Akpabio!"

A ranar Alhamis, babbar kotun tarayya da ke Lokoja ta bayar da umarnin dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) daga karɓa ko aiki da kowace takardar koke da ke neman yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye.

Kara karanta wannan

Kiranye daga majalisa: Sanata Natasha ta fadi aɓin da take tsoro

Sai dai a ranar Juma’a, kotun ta soke wannan umarni, tana mai cewa ‘yan ƙasa na da haƙƙin da kundin tsarin mulki ya basu na yin kiranye ga duk wani ɗan majalisa idan suna buƙatar hakan.

Natasha ta ci gaba da zargin Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya ta sake fitar da bayanai kan zargin da take yi wa Sanata Godswill Akpabio kan yunƙurin yin lalata da ita.

Sanata Natasha ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawan ya taɓa nuna mata alamar cewa yana son yin lalata a cikin harabar majalisar.

Ta nuna cewa majalisar dattawan na azabtar da ita ne saboda ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng