Dokar Ta Baci: Ministan Tinubu Ya Caccaki Kwankwaso, Ya Fadi Gazawarsa

Dokar Ta Baci: Ministan Tinubu Ya Caccaki Kwankwaso, Ya Fadi Gazawarsa

  • Ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi wa Rabiu Musa Kwankwaso martani kan sukar dokar ta ɓaci a Rivers
  • Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki tsohon gwamnan na jihar Kano wanda ya bayyana a matsayin mai ƙaramin sani kan doka da harkokin mulki
  • Ya buƙaci Kwankwaso da ya mayar da hankali wajen warware rikicin masarautar Kano wanda ya ƙara dagulawa ta hanyar yaronsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya soki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.

Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki Kwankwaso ne kan wata magana da ya yi game da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Bayanai sun fito kan zargin ba kowane dan majalisa $5000 don Amincewa da dokar ta baci

Ata ya caccaki Kwankwaso
Yusuf Abdullahi Ata ya caccaki Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Umar Bichi
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Seyi Olorunsola, ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Abdullahi Ata ya ba Kwankwaso shawara

Ministan ya shawarci Kwankwaso da ya riƙe ra’ayinsa, yana mai cewa shawarar da shugaban ƙasa ya yanke an yi ta ne domin tabbatar da kwanciyar hankali, ci gaban dimokuraɗiyya, da kuma tsaro a ƙasa.

Ministan ya bayyana cewa ya kamata jama’a su fahimci cewa matakin sanya dokar ta ɓacin, wani abu ne da ya zama tilas don daidaita doka da oda a jihar Rivers, wacce ta daɗe tana fama da rikicin siyasa.

Har ila yau, ministan ya yabawa majalisar tarayya da ta ƙunshi majalisar dattawa da majalisar wakilai, saboda amincewarsu cikin gaggawa da kuma kishin ƙasa dangane da wannan matsaya ta shugaban ƙasa.

"Ƴan majalisa na yanzu ƙwararru ne masu basira, waɗanda za su iya gudanar da cikakken bincike kan rahotannin tsaro don daƙile ƙarin rikici, saɓanin Kwankwaso, wanda bai taka rawar gani ba a tsawon shekarun da ya yi a majalisar dattawa."

Kara karanta wannan

Jonathan ya tsoma baki kan dakatar da Fubara, ya fadi illar hakan ga Najeriya

- Yusuf Abdullahi Ata

Ministan Tinubu ya caccaki Kwankwaso

Ministan ya ƙara da cewa abin takaici ne cewa Kwankwaso yana da ƙaramin sani kan fahimtar doka da mulki.

Ya shawarce shi da ya mayar da hankalinsa wajen warware rikicin da ke ci gaba da dabaibaye masarautar Kano, wanda ya ƙara dagulawa ta hanyar yaronsa na siyasa, Gwamna Abba Kabir Yusuf.

“A bayyane yake cewa Shugaba Tinubu ya yi aiki ne cikin iyakar dokar kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya ba shi ikon aiwatar da matakan dokar ta-ɓaci."
"Duk wata jiha da ke fama da rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya kamata ta ɗauki darasi ta magance matsalolinta."

- Yusuf Abdullahi Ata

Jonathan ya soki dakatar da Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya nuna takaicinsa kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Goodluck Jonathan ya bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami'an gwamnati abu ne wanda zai shafawa ƙasar nan baƙin fenti a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng