Kurunkus: Bayanai Sun Fito kan Zargin ba Kowane Dan Majalisa $5000 don Amincewa da Dokar Ta Baci

Kurunkus: Bayanai Sun Fito kan Zargin ba Kowane Dan Majalisa $5000 don Amincewa da Dokar Ta Baci

  • Majalisar wakilai ta nesanta kanta daga zargin cewa ta karɓi cin hanci kafin amincewa da dokar ta ɓaci a jihar Rivers
  • Mataimakin kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa babu komai a cikin zargin face tsabagen ƙarya da makirci
  • Philip Agbese ya nuna cewa majalisar ta amince da dokar ta ɓacin ne saboda kishin ƙasa da kuma dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi martani kan zargin an ba kowane ɗan majalisa dala 5,000 don amincewa da buƙatar Bola Tinubu kan dokar ta ɓaci a Rivers.

Majalisar wakilan ta ƙaryata zargin ba ta cin hanci domin amincewa da matakin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Majalisa ta musanta zargin cin hanci
Majalisar wakilai ta musanta zargin karbar cin hanci kan dokar ta baci a Rivers Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Mataimakin kakakin majalisar, Hon. Philip Agbese (Benue, APC), ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Abuja ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Na yi mamaki": 'Dan majalisa ya magantu kan karbar cin hanci don dokar ta baci a Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta musanta zargin karɓar cin hanci

Ya bayyana zargin a matsayin ƙarya, makirci wanda ko kaɗan ba ya da tushe ballantana makama.

A cewarsa, shawarar da majalisar ta yanke a ranar Alhamis game da dokar ta-ɓaci a Rivers, an yita ne da kishin ƙasa da kuma nufin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

"Zargin cewa an bai wa ƴan majalisa dala 5,000 domin su amince da wannan matsaya ba adalci ba ne ga majalisar."
“Duk wani raɗe-raɗi da ke cewa wani ya karɓi kuɗi domin rabawa ƴan majalisa ba komai ba ne face ƙarya da makirci. ƴan adawa su daina ƙin ganin abubuwan alheri da muke yi dare da rana domin ci gaban ƙasar nan."
"A kowane lokaci, ba mu taɓa shiga wata harkar cin hanci ko badaƙala ba dangane da ayyana dokar ta ɓaci."
"An yanke wannan shawara ne bayan dogon nazari kan halin tsaro da rikicin siyasa a jihar Rivers, domin cika nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mana na kare zaman lafiyar ƙasa."

Kara karanta wannan

"Me yasa ba ka sa a Legas ba?" An tunkari Tinubu da tambaya kan dokar ta ɓaci

"Maganar cewa an bai wa ƴan majalisa cin hanci tatsuniya ce kawai da ake ƙirƙira domin ɓata gaskiya da haddasa rashin jituwa a ƙasar nan."
"Zargin cin hancin wani yunƙuri ne maras tushe da nufin ɓata sunan majalisar, don haka a ɗauke shi a matsayin wasan kwaikwayo na siyasa kawai."

- Philip Agbese

Ya ƙara da cewa, a matsayinsu na ƴan majalisar da ke da sha’awar zaman lafiya da jin daɗin al’ummar jihar Ribas, sun amince da dokar ta-ɓaci ne saboda kishin ƙasa, ba don samun kuɗi ba kamar yadda ake zargi.

Jonathan ya soki dakatar da Fubara

A baya rahoto ya zo cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da matakin dakatar da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

Jonathan wanda ya yi mulki na shekaru biyar ya bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami'an gwamnati abu ne wanda zai ɓata sunan ƙasar nan a idon duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng