Jonathan Ya Tsoma Baki kan Dakatar da Fubara, Ya Fadi Illar Hakan ga Najeriya

Jonathan Ya Tsoma Baki kan Dakatar da Fubara, Ya Fadi Illar Hakan ga Najeriya

  • Goodluck Jonathan ya yi martani kan matakin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da wasu jami'an gwamnati
  • Tsohon shugaban ƙasa ya yi Allah wadai da matakin, inda ya ce hakan zai shafawa Najeriya baƙin fenti a idon duniya
  • Tsohon shugaban ƙasan ya nuna cewa ya ji takaicin yadda aka dakatar da zaɓaɓɓun jami'an gwamnati daga muƙamansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi magana kan dokar ta ɓaci da dakatar da jami'an gwamnati da shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers.

Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar, ya na mai cewa wannan matakin na iya ɓata sunan ƙasar nan.

Jonathan ya soki dakatar da Gwamna Fubara
Jonathan ya ji takaicin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara Hoto: Goodluck Jonathan, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jonathan ya ji takaicin dakatar da Fubara

Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taron gidauniyar Haske Satumari da aka gudanar a Abuja a ranar Asabar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Abin da ya faru bayan Atiku Abubakar ya kammala jawabi a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan ya ce ya ji takaici ganin an cire zaɓaɓɓun shugabanni daga muƙamansu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ra’ayinsa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar ta yankin kudu maso kudu mai arziƙin mai.

Shugaban ƙasan ya kuma dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan zababbun ƴan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Jonathan ya tsoma baki a batun Rivers

Sai dai, yayin da yake bayyana ra’ayinsa kan rikicin siyasar da ke faruwa a Rivers, Jonathan ya ce ba ɗabi’ar tsofaffin shugabanni ba ce su tsoma baki a harkokin siyasa domin ka da a ƙara dagula lamarin.

Ya nuna cewa yana da mahimmanci a lura cewa mutuncin ƙasa da yawan hannun jarin da ke shigowa na da alaƙa da matakan da ɓangaren zartaswa, majalisar dokoki da ɓangaren shari’a ke ɗauka.

A cewarsa, ya ga ya zama wajibi ya yi tsokaci kan lamarin ne saboda kiraye-kirayen da ƴan Najeriya da dama suka yi masa, ganin cewa shi babban ɗa ne ga yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi

Ya kuma yi tir da yadda wani mutum guda zai iya umartar ɓangaren shari’a kan abin da za su yi, yana mai cewa hakan na rage wa mutane ƙwarin gwiwar samun adalci daga ɓangaren shari'a.

"Waɗannan matakai da manyan jiga-jigan ɓangaren zartaswa da majalisar dokoki ke ɗauka su na ɓata sunan ƙasar nan."

- Goodluck Jonathan

Ɗan majalisa ya musanta karɓar cin hanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin ƴan majalisar wakilan Najeriya ya musanta zargin cewa an ba su cin hanci kafin su amince da dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Yusuf Shittu Galambi ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa sun karɓi cin hanci babu komai a cikinsu face tsabagen ƙarya.

Ya bayyana cewa sun amince da dokar ta ɓacin ne saboda kishin ƙasa da kuma ceto dimokuraɗiyya a jihar Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng