Bayan Barazanar Dokar Ta Baci a Kano, Aminu Ado Bayero Ya Gana da Wike

Bayan Barazanar Dokar Ta Baci a Kano, Aminu Ado Bayero Ya Gana da Wike

  • Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gana da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kafin halartar taron yaye dalibai a Jami’ar Calabar
  • Jami’ar za ta yaye dalibai 13,610 a bikin kammala zangon karatun 2024/2025 da ake gudanarwa daga 17 zuwa 23 ga watan Maris
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar jami’ar za ta karrama fitattun mutane shida da digirin girmamawa a yayin bikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gana da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a wata ganawa ta sirri kafin halartar bikin yaye dalibai a Jami’ar Calabar.

Jami’ar Calabar ta shirya bikin yaye dalibai karo na 37 a karshen zangon karatu na shekarar 2024/2025, wanda aka fara daga 17 zuwa 23 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

Aminu Ado
Aminu Ado ya gana da Wike a Calabar Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

Legit ta hango hoton mai martaba Aminu Ado na ganawa da Nyesom Wike ne a cikin wani sako da shafin Masarautar Kano ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Aminu Ado ya tattauna da Wike?

Har yanzu bayanai ba su fito a kan abubuwan da Ministan Abuja ya tattauna da mai martaba Aminu Ado Bayero ba.

Sai dai an hango su suna magana su biyu, kuma ana tsammanin za a karrama Wike da wasu manyan jami'ai a jami'ar.

Ganawar Wike da Aminu Ado Bayero ta cigaba da daukar hankali ne kasancewar sun hadu bayan APC ta yi barazanar sanya dokar ta baci a Kano.

Za a yaye dalibai 13,610 a jami'ar Calabar

Shugabar jami'ar, Farfesa Florence Obi ta bayyana cewa jimillar dalibai 13,610 ne za su kammala karatu a jami’ar, ciki har da 66 da suka samu digiri mai daraja ta daya.

The Guardian ta wallafa cewa dalibai 181 za su karɓi takardar shaidar difloma, 11,725 za su sami digiri na farko, 876 za su kammala digirgi, 572 kuma za su karɓi digirin digirgi.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Haka kuma, dalibai 249 za su sami difloma ta digiri na biyu, yayin da wasu bakwai za su karɓi difloma ta musamman bayan digiri na uku.

Kaddamar da sababbin ayyuka a jami’ar

Shugabar jami’ar ta ce a yayin bikin, za a kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka kammala karkashin jagorancinta.

Daga cikin ayyukan da za a bude akwai katafaren dakin taro na musamman, ginin Kwalejin Ilimi, da sabuwar tashar kashe gobara tare da motar kashe gobara.

Bayar da digirin girmamawa ga fitattun mutane

Farfesa Obi ta bayyana cewa jami’ar za ta karrama manyan mutane shida da digirin girmamawa bisa gudunmawar da suka bayar ga al’umma.

Daga cikin wadanda za a karrama akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Bassey Otu, da matar Shugaban Majalisar Dattawa, Ekaete Uloma Godswill Akpabio.

Haka kuma, za a karrama Manjo Janar Moses Bisong Obi (Mai ritaya), Mai shari’a Emmanuel Akomaye Agim, da fitaccen ɗan kasuwa, Prince Arthur Eze.

Kara karanta wannan

'Me shirunsa ke nufi?' An taso Kwankwaso a gaba game da dokar ta ɓaci a Rivers

Pantami ya yi magana kan sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya koka kan yadda rikicin sarautar Kano ya ki karewa.

Haka zalika malamin ya yi magana kan yadda matsaloli ke cigaba da karuwa a Arewacin Najeriya ba tare da magance su ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng