Duniyar Fina Finan Najeriya Ta Yi Rashi, Fitacciyar Jaruma Ta Rasu bayan Mata Tiyata
- Jarumar masana'antar shirya fina-finai, Nollywood, Nkechi Nweje ta riga mu gidan gaskiya tana da shekara 51 a duniya
- Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da jinya ta ɗan lokaci sakamakon tiyatar da aka mata a watan Nuwamba, 2024
- Tuni dai abokan aikinta a harkar Nollywood suka fara alhini da tura saƙonnin ta'aziyya bisa wannan rashi da suka yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - An tabbatar da rasuwar fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Nkechi Nweje, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Wannan labari ya girgiza masana’antar shirya fina-finai ta Kudancin Najeriya, inda abokan aikinta da masoya suka fara nuna alhininsu kan rashin jaruma mai ƙwazo da sadaukarwa.

Asali: Instagram
Shugaban kamfanin shirya fina-finai, Stanley Ajemba, wanda aka fi sani da Stanley Ontop, shi ne ya tabbatar da rasuwarta a ranar Asabar a shafinsa na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masana'antar Nollywood ta yi rashi
Ajemba ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai ƙwazo, kishin sana’ar da take yi, sannan kuma abokiyarsa ta kud da kud da yake alfahari da ita.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Ajemba ya bayyana yadda labarin mutuwarta ya girgiza shi, yana mai cewa har yanzu kamar mafarki ne a gare shi.
Ajemba ya ce:
"Masana'antar Nollywood na cikin alhini bayan rasuwar ɗaya daga cikin jarumanmu masu ƙwazo, @nkechi.nweje, bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Tun safiya ban iya wallafa komai ba saboda ji na ke kamar mafarki na ke yi. Ezigbo Nwanyi Onitsha."
Jaruma Nweje tana da ƙima a Nollywood
Ya kuma tuna yadda suka yi hira ta ƙarshe da marigayiyar a lokacin rikicinsa da wata shahararriyar jaruma mai suna Queenth, inda ta ba shi shawarar ya dakata.
"Ki huta lafiya, uwargida. Ƙawata ta kusa, wadda kullum take kirana tana ba ni shawara. Maganarta ta ƙarshe da ni ita ce lokacin rikici na da Queenth, ta ce mani, ‘Ontop, ka dakata.’ Har yanzu ban kara magana ba.”
Takaitaccen bayani kan jaruma Nweje
Marigayiya Nkechi Nweje ta rasu ta bar mijinta, Dr. Azuibuike Nweje, da ‘ya’ya shida, waɗanda suka shiga cikin jimami bayan wannan babban rashi.
Ta fito a fina-finai da dama a Nollywood, amma dai ta fi shahara wajen taka rawar uwa, dattijuwa, ko kuma mace mai hikima da basira.
Ta kasance jaruma mai ƙwarewa da iya daidaita kowace irin rawa da aka ba ta a fina-finai.
Marigayiya Jarumar ta fito ne daga jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, kuma an haife ta ranar 6 ga watan Yuni, 1964.
Wata majiya daga iyalanta ta bayyana cewa Nkechi Nweje ta rasu ne sakamakon tiyatar da aka mata a watan Nuwamba, 2024, wanda ta fara warkewa amma kuma ajali ya riske ta.
Jarumin Nollywood ta riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, kun ji cewa Jarumi Columbus Irisoanga wanda ke yawan fitowa a matsayin boka a fina-finan Nollywood ya riga mu gidan gaskiya.
Mutuwar Irisoanga na zuwa ne kwana ɗaya bayan sanar da rasuwar matashiya a masana'antar shirya fina-finan Nollywood.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng