"Na Yi Mamaki": 'Dan Majalisa Ya Magantu kan Karbar Cin Hanci don Dokar Ta Baci a Rivers

"Na Yi Mamaki": 'Dan Majalisa Ya Magantu kan Karbar Cin Hanci don Dokar Ta Baci a Rivers

  • Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gwaram a Jigawa, ya taɓo batun zargin ba ƴan majalisu cin hanci kan dokar ta ɓaci a Rivers
  • Yusuf Shittu Galambi ya musanta zargin cewa na ba su na goro domin su amince da dokar ta ɓacin da shugaba Bola Tinubu ya sanya
  • Ɗan majalisar ya bayyana cewa sun amince da dokar ta ɓacin ne domin kishin ƙasa da kare dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram a jihar Jigawa, Yusuf Shittu Galambi, ya yi magana kan zargin karɓar cin hanci kafin amincewa da dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Ɗan majalisar ya ƙaryata zargin cewa ƴan majalisar tarayya sun karɓi cin hanci don su goyi bayan ayyana dokar ta-ɓaci da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Bayanai sun fito kan zargin ba kowane dan majalisa $5000 don Amincewa da dokar ta baci

Dan majalisa ya yi magana kan cin hanci
Shittu Yusuf Galambi ya ce ba a ba su cin hanci ba don amincewa da dokar ta baci a Rivers Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Yusuf Shittu Galambi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 22 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganganun Yusuf Shittu Galambi sun zo ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan dokar ta ɓacin, inda wasu ƙungiyoyi ke zargin cewa an ba majalisar tarayya cin hanci don amincewa da matakin.

Ɗan majalisa ya musanta karɓar cin hanci

Sai dai a sanarwar da ya fitar, Yusuf Shittu Galambi ya musanta iƙirarin cewa an yi wa ƴan majalisa tayin kuɗi ko kuma an matsa musu lamba don su amince da matakin na shugaban ƙasa.

A cewarsa, yawancin ƴan majalisar sun amince da wannan mataki ne saboda kishin dimokuradiyya da kuma kare muradun al’ummar jihar Rivers.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa shawarar da majalisar tarayya ta yanke ta dogara ne a kan kishin kasa, haɗin kan ƴan siyasa, zaman lafiya da kuma kare tsare-tsaren dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Jonathan ya tsoma baki kan dakatar da Fubara, ya fadi illar hakan ga Najeriya

"Na yi mamakin rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai, musamman ƙaryar da ake yaɗawa a kanmu, kan cewa wai mun karɓi kuɗi ko kuma an matsa mana lamba don mu amince da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka a jihar Rivers."
"Yawancin ƴan majalisar sun goyi bayan ƙoƙarin shugaban ƙasa na ceton dimokuradiyya da kare Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ke fuskantar matsin lamba daga wasu mambobin majalisar dokokin jihar Rivers, wanda ka iya kai wa ga tsige shi daga muƙaminsa."
"Ya kamata ƴan Najeriya su fahimci rawar da majalisar tarayya ta taka wajen rokon shugaban ƙasa da ya kafa kwamitin sulhu na manyan ƴan kasa kafin wa’adin dokar ta-ɓaci ta watanni shida ya ƙare."
"Saɓanin ra’ayin ƴan adawa, ƙungiyoyin farar hula da wasu masu sukar lamarin, mu a majalisar tarayya mun ɗauki wannan mataki ne daga mahangar kishin kasa, zaman lafiya, tare da burin kare dimokuradiyya."
"Saboda haka, ina kira ga ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da su ba zaman lafiya dama, ta hanyar barin shugaban ƙasa ya yanke matsaya mafi dacewa don warware wannan rikici ta hanyar tattaunawa da haɗin kai."

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan Lakurawa cikin azumi, an samu asarar rayuƙa

- Yusuf Shittu Galambi

Majalisa ta amince da dokar ta ɓaci a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Majalisar ta amince da buƙatar shugaban ƙasan ne bayan ta gudanar da wani zaman sirri a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng