An ba Kowane Sanata $15,000 kafin Su Amince da Dokar Ta Ɓaci a Ribas? Bayanai Sun Fito

An ba Kowane Sanata $15,000 kafin Su Amince da Dokar Ta Ɓaci a Ribas? Bayanai Sun Fito

  • Shugaban Majalisar Dattawa ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa an ba kowane sanata Dala 15,000 domin amincewa da dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Mai magana da yawun shugaban majalisar, Hon. Eseme Eyiboh ya ce an kirkiri jita-jitar ne domin ɓata wa Godswill Akpabio suna kurum
  • Ya ce Akabio ya shirya buɗa baki kamar yadda ya saba amma babu wasu Daloli da ya rabawa sanatoci domin amincewa da dokar ta -ɓacin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin da ake yi cewa ya bai wa sanatoci cin hanci na $15,000 don su goyi bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana wannan zargi a matsayin wani ɓangare na yaƙin ƙiyayya da yake zargin ana yi masa tun da ya hau kujerar shugaban Majalisa.

Kara karanta wannan

"Me yasa ba ka sa a Legas ba?" An tunkari Tinubu da tambaya kan dokar ta ɓaci

Godswill Akpabio.
Akpabio ya ƙaryata zargin bai wa sanatoci $15,000 don amincewa da dokar ta-ɓaci a jihar Rivers Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan shi ne karo na farko da Akpabio ya fito ya yi magana tun bayan yaɗuwar jita-jitar a kafafen sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin rabawa sanata Dala 15,000

Jita-jitar da ake yaɗawa ta zarge shi da jagorantar rabon kuɗin a gidansa da ke Maitama, Abuja, yayin buda bakin azumi da ya shirya tare da sanatoci.

Rahoton ya nuna cewa ana zargin Shugaban Majalisar Dattawa da raba $5,000 ga sanatoci a ranar Talata, sannan daga baya ya ƙara masu $10,000 a ranar Laraba, wato a gabanin jefa ƙuri’a kan ayyana dokar ta-baci.

Sai dai, shugaban Majalisar Dattawan, Akpabio, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Hon. Eseme Eyiboh, ya musanta zargin.

"Tun lokacin da Sanata Godswill Akpabio ya hau kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, ya saba shirya buda baki.
"Ya yi haka a bara, kuma ya yi wannan shekarar, to me ya sa aka mayar da hakan zuwa wata jita-jita?"

Kara karanta wannan

Fubara: Jigon PDP ya fita daban da sauran ƴan jam'iyya kan sanya dokar ta-ɓaci

- In ji Eyiboh.

Majalisa ta amince da dokar ta ɓaci a Ribas

Idan ba ku manta ba Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas a zamanta na ranar Alhamis.

Haka nan kuma Majalisar Wakilai ta amince da sanya dokar ta ɓacin, duk ta hanyar kaɗa kuri'ar murya.

Jim kaɗan bayan haka aka fara yaɗa jita-jitar cewa an rabawa sanatoci Dala 15,000 domin amincewa da bukatar Tinubu.

Majalisar Dattawa.
Shugaban Majalisar Dattawa ya musanta ba kowane sanata Dala 15,000 Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Da gaske an raba wa sanatoci $15,000?

Mista Eyiboh ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa Akpabio ya rabawa sanatoci waɗannan maƙudan daloli, a cewarsa an kirƙiri labarin ne don ɓata masa suna.

Eyiboh ya ƙara da cewa:

"Me zai sa Akpabio ya raba wa sanatoci Dalolin Amurka? Na san an yi buda baki, amma ban san da wani rabon $5,000 ko $10,000 ba.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Wannan labari kawai an ƙirƙire shi ne don a ƙara ɓata masa suna."

Majalisa ta yi gyara a dokar ta ɓaci

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta yi gyare-gyare a dokar ta ɓacin daBola Tinubu ya ƙaƙaba a jihar Ribas kafin amincewa da ita.

Yan majalisar sun dage kan cewa shugaban riko da aka nada a Ribas zai rika kai rahoto kai tsaye ga majalisar tarayya, ba ga majalisar zartarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng