Mummunan Rikici Ya Barke, Gwamna Ya Tara Sarakuna bayan Sanya Dokar Hana Fita
- Gwamnan Osun ya sake kakabawa garuruwan Ifon da Ilobu dokar hana fita daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe
- Ademola Adeleke ya umarci sarakunan Olufon da na Olobu da sauran masu ruwa da tsaki su halarci taron yin sulhu
- Rikici ya sake barkewa tsakanin al’ummomin biyu, inda wani tsohon kansila daga Ifon, mai suna Azeez, ya rasa ransa
- An kona wasu gidaje yayin fadan, inda kowane bangare ke zargin dayan da fara ta da rikicin da tayar da tarzoma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya dauki muhimmin mataki bayan barkewar rikici a jihar da ya sanadin rai.
Gwamna Adeleke ya sake kakabawa garuruwan Ifon da Ilobu dokar hana fita na tsawon sa’o’i 12 sakamakon sake barkewar rikici a jihar Osun.

Asali: Twitter
Gwamna ya kira taron gaggawa da sarakuna
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai, Kolapo Alimi da jaridar Punch ta leko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, an bayyana cewa dokar hana fitar zata fara ne daga 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.
Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya umurci a gudanar da taron gaggawa tare da sarakunan garuruwan biyu da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin.
Sanarwar ta ce:
“Don haka, Gwamnan ya umarci a tsawaita dokar daga 10:00 na dare zuwa 4:00 na safe zuwa 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe daga yau.
“Gwamnan ya kuma umarci jami’an tsaro da su ci gaba da sintiri na awa 24 domin hana duk wani abu da ka iya tayar da hankali.
“Haka kuma, an umurci a gudanar da taron sulhu tsakanin Olufon na Ifon da Olobu na Ilobu da sauran masu ruwa da tsaki daga kowanne bangare."

Asali: Facebook
Rokon da Gwamna Adeleke ya yi ga al'ummarsa
Gwamna Adeleke ya bukaci jama’ar garuruwan biyu da sarakunansu da su zauna lafiya, ya gargadi masu haddasa rikici cewa za a hukunta su.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta dakatar da dokar hana fita kwanan nan saboda dawowar zaman lafiya, amma rikici ya sake faruwa.
Haka kuma, yayin fadan, gidaje da dama sun kone kamar yadda rahotanni suka bayyana daga yankin, cewar rahoton Tribune.
Mai magana da yawun Olufon na Ifon, Yusuf Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi mutanen Ilobu da kai harin tun farko.
Sai dai Otun Jagun na Ilobu, Adegoke Ogunsola, ya karyata zargin, ya na cewa mutanen Ifon ne suka fara kai hari wanda ya jawo asara.
Osun: Rikici ya yi sanadin mutuwar tsohon kansila
Kun ji cewa an samu hatsaniya bayan ɓarkewar rigima tsakanin mutanen kauyukan Ifon da Ilobu a jihar Osun.
Yayin rikicin, an kashe tsohon kansila da wasu mutane da ba a tantance lokacin da mutanen garuruwan biyu suka fara kai wa juna hare-hare da ƙona gidaje.
Ba a tantance cikakken yadda mutumin ya mutu ba, amma wani mazaunin Ifon ya ce an tabbatar da rasuwarsa a asibitin UNIOSUN da ke Osogbo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng