Allahu Akbar: Bayan Fama da Jinya, Shugabar Karamar Hukuma Ta Rasu a Ramadan
- Shugabar karamar hukumar Ayobo-Ipaja, Bolatito Shobowale, ta rasu bayan doguwar jinya, lamarin da ya jefa al’umma a alhini da jimami
- Mai rikon mukamin shugabar, Otunba Ladi Oluwaloni, ya tabbatar da mutuwarta, yana cewa lamarin ya girgiza shi matuka kuma sauran al'umma
- An yaba da irin gudunmawar Shobowale wajen ci gaban unguwanni, kiwon lafiya, da karfafa al'umma tun lokacin da take kan mulki a jihar Legas
- Mutane da dama sun bayyana takaicinsu bisa rashin shugaba mai hangen nesa, suna addu’ar Allah ya jikanta da rahama a watan nan na azumi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Shugabar karamar hukumar Ayobo-Ipaja a jihar Lagos, Hajiya Bolatito Shobowale, ta rasu.
Marigayiyar ta rasu ne bayan ta sha fama da doguwar jinya wanda lamarin ya girgiza al’ummar yankin sosai.

Asali: Twitter
An yi rashin shugabar karamar hukuma a Lagos
Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar ta sha fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba, kafin ta ce ga garinku, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai rikon mukamin shugaban karamar hukumar, Otunba Ladi Oluwaloni (OLO 1), ya tabbatar da mutuwar a cikin wata gajeriyar takaitacciyar jawabi mai sosa rai.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya nada Oluwaloni kwanan nan a matsayin mai rikon kwarya saboda rashin lafiyar Shobowale.
Sanarwar ta ce:
“Hon. Chif Shobowale ba shugaba kadai ba ce ba; uwa ce, jagora ce kuma ginshiki ga mutane da dama.
"Ta sadaukar da rayuwarta wajen inganta yankin Ayobo-Ipaja, inda ta nuna soyayya da jajircewa a kowane fanni."

Asali: Getty Images
An yaba da gudunmawar da marigayiyar ta bayar
An yaba da rawar da marigayiyar ta taka wajen inganta ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya da bunkasa rayuwar al’umma.
Oluwaloni ya ce abubuwan da ta bari na kishin kasa da gaskiya za su ci gaba da zamo wa sababbin shugabanni darasi.
Ya ce:
“Ina mika ta’aziyyata ga iyalanta, abokanta da daukacin wadanda suka ji radadin wannan babban rashi.
"Ko da mun yi bankwana da ita, tasirin ta zai ci gaba da zama a zukatan wadanda ta taba rayuwarsu.”
Al'umma sun yi jimamin mutuwar shugabar karamar hukuma
Al’ummar Ayobo-Ipaja sun bayyana bakin cikinsu, suna tuna yadda take da saukin kai da jajircewa wajen kare muradun talakawa.
Yayin da ake shirin jana’izarta, daukacin al’ummar yankin na ci gaba da jimamin rashin shugabar mai nagarta da hangen nesa.
Mutane sun bayyana marigayiyar a matsayin mutumiyar kirki wacce ta ba da gudunmawa sosai wurin ci gaban al'ummar yankin.
Attajiri kuma malami a Kano ya rasu
Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta yi rashin wani shahararren malami kuma attajiri wanda shi ne shugaban kamfanin Mainsara & Sons.
Marigayin mai suna Alhaji Nasiru Ahali, ya rasu ya na da shekaru 108 a duniya kamar yadda ɗansa, Aminu Ahali, ya tabbatar ya na mai cewa ya rasu a wani asibiti da ke Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar Alhaji Nasiru Ahali a matsayin babban rashi ga Kano, Najeriya da al'ummar Musulmi duka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng