"Ka da a Ɗora Mun Laifi": Gwamna Fubara Ya Cire Tsoro, Ya Ƙaryata Kalaman Tinubu
- Gwamna Siminalayi Fubara ya karyata zarge-zargen Bola Tinubu na cewa ya rushe majalisar dokokin Rivers ba tare da sake gina ta ba
- Fubara ya ce ya dauki matakai don kare albarkatun mai na jihar, kuma sabuwar majalisar dokoki ta kusa kammaluwa da kashi 80%
- Ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da haddasa rikici a jihar ta hanyar furta kalaman da suka tada hankulan ‘yan kabilar Ijaw
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ya mayar da martani kan zarge-zargen da Bola Tinubu ya yi a jawabinsa na ayyana dokar ta-baci.
A cewar rahoton Legit.ng Hausa, shugaba Tinubu ya dakatar da Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar na watanni shida tare da naɗa shugaban riko a jihar.

Asali: Twitter
Zarge-zargen da Tinubu ya yi wa Fubara
A jawabinsa, shugaban kasar ya ce Fubara ya rushe majalisar dokokin Rivers tun 13 ga Disamba, 2023, amma har yanzu bai gina sabuwa ba, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, ya kuma zargi Fubara da hana majalisar yin aiki, yana mai cewa hakan ya sa babu cikakken gwamnati a jihar Rivers.
Tinubu ya ce wasu 'yan bindiga sun yi barazanar kai hari kan abokan hamayyar gwamna, amma Fubara bai yi wani mataki na hana su ba.
Shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa an samu fashewar bututun mai a jihar ba tare da Gwamna Fubara ya dauki mataki ba.
Fubara ya karyata kalaman shugaba Tinubu
Sai dai, a martaninsa ta hannun kakakinsa, Nelson Chukwudi, Fubara ya ce duka wadannan zarge-zargen na shugaba Tinubu ba su da tushe.
Sanarwar ta ce:
"Da farko, ya na da muhimmanci a fayyace cewa Gwamna Fubara ba shi da wata alaka da barazanar ‘yan bindiga kuma bai ba da wata alaka ta nesa ko ta kusa da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin mai a jihar."
Fubara ya kuma karyata ikirarin Tinubu na cewa ya bar ginin majalisar a wofance, ya yi martani da cewa ginin sabuwar majalisar ya kusa kammaluwa da kashi 80%.
Dakataccen gwamnan ya ce wasu masu ba shugaban kasa shawara sun ba shi bayanan da ba su dace ba kan halin da ake ciki a jihar Rivers.
"Da farko, mun yi watsi da waɗannan maganganu saboda mun san waɗanda ke da alhakin samar da irin wannan bayanin ga shugaban kasa ba su fada masa gaskiyar abin da ke faruwa ba.
"Amma yanzu muna ganin ya zama dole mu gyara bayanan domin kawar da kuskuren fahimta da irin waɗannan labarai ke haifarwa a zukatan ‘yan Najeriya."

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
- Inji Gwamna Fubara.
Gwamna Fubara ya lissafo matsalolin Wike
Fubara ya danganta wasu daga cikin rikicin jihar da kalaman ministan Abuja, Nyesom Wike, kan kabilar Ijaw.
Ya ce Wike ya yi kalaman raini kan ‘yan kabilar Ijaw, amma ya ki bayar da hakuri duk da koke-koken da aka yi masa.
Ya kuma lissafo wasu lokuta da magoya bayan Wike suka tayar da hatsaniya, yana mai cewa nasa magoya bayan sun kasance cikin nutsuwa da lumana.
Fubara ya ce tun farkon mulkinsa ya dauki matakai don kare albarkatun man fetur na jihar daga masu tada zaune tsaye.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa na bayar da gudunmawa wajen bunkasa tsaro da samar da kayan aiki ga hukumomin tsaro.
Zababben gwamnan na Rivers ya ce matsayinsa na kare zaman lafiya ne ya taimaka wajen karuwar kudaden shiga daga jihar zuwa asusun tarayya.
Asali: Legit.ng