'Yan Majalisun Arewa Sun Dunkule Waje 1, Sun Fadi Matsayarsu kan Dokar Ta Baci a Rivers
- Ƙungiyar ƴan majalisar wakilai daga Arewacin Najeriya ta nuna goyon bayanta kan dokar ta ɓacin da aka sanya a jihar Rivers
- Shugaban ƙungiyar, Alhassan Doguwa, ya bayyana cewa sun yi na'am da matakin da Bola Tinubu ya ɗauka kan rikicin siyasar Rivers
- Ya bayyana cewa shugaban ƙasan yana da hurumin sanya dokar duba da irin damar da kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ba shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƴan majalisar wakilai daga Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan dokar ta ɓacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.
Ƙungiyar ƴan majalisar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na sanya dokar ta ɓacin.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma jagoran ƴan majalisa daga Arewa, Ado Doguwa, ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata ne dai shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar.
Ƴan majalisun Arewa sun goyi bayan Tinubu
Ƴan majalisar sun ce ba za su yarda ƴan ta’adda da ƴan daban siyasa su ci gaba da lalata muhimman kayayyakin ƙasa, wanda hakan zai iya shafar tattalin arzikin ƙasar nan.
"Dangane da muhawarar da ke gudana kan dokar ta ɓaci a jihar Rivers, muna buƙatar bayyanawa a fili cewa matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka ya dace, kuma ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa."
“A matsayina na shugaban wannan ƙungiya, ina mai bayyana cewa a madadin ƴan majalisar arewa na majalisar wakilai ta 10, muna ba da cikakken goyon baya ga dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa ya ayyana, bisa ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi a ƙarƙashin sashe na 305."
- Alhassan Ado Doguwa
Alhassan Doguwa ya ce majalisar tarayya ba za ta yarda wannan mataki na shugaban ƙasa ya gaza ba, domin yana kan doka kuma an ɗauke shi ne don samar da tsaro da daidaita al’amuran siyasa a jihar.
'Yan Majalisar Arewa sun nuna yatsa ga ƴan adawa
Ya kuma zargi ƴan adawa da ƙoƙarin siyasantar da batun, yana mai cewa:
"Ƴan adawa suna ƙoƙarin juya wannan batu ne kawai don dalilai na siyasa. Duk da cewa muna da masaniya kan dokokin kundin tsarin mulki da tasirin da ke tattare da hakan, ba za mu yi watsi da matsalar tabarbarewar doka da oda da ke gudana a jihar Rivers ba."
Doguwa ya ƙara da cewa ƴan majalisar tarayya daga Arewa sun amince da wannan mataki ne domin ya yi da daidai da nufi kare dimokuraɗiyya a Najeriya.
Majalisa ta amince da dokar ta ɓaci a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta amince da dokar ta ɓacin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Kara karanta wannan
Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi
Majalisar ta amince da dokar ne biyo bayan wani zama na sirri da ta yi kan buƙatar da shugaban ƙasan ya aike mata ta neman amincewa da matakin da ya ɗauka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng