Rikicin Rivers: Abin da Ya Faru bayan Atiku Abubakar Ya Kammala Jawabi a Abuja
- Alhaji Atiku Abubakar ya ci gaba da fafutukar ganin an janye dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙaƙaba a jihar Ribas
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya tattauna da tsohon gwamnan Ribas jim kaɗan bayan barin wurin taron haɗin guiwar ƴan adawa a Abuja
- Atiku, Malam Nasir El-Rufai da manyan ƴan adawa sun bukaci Tinubu ya janye dokar da ya ayyana, sannan a maida Gwamna Fubara kan mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya fara ƙoƙarin tuntuɓar manyan jihar Ribas kan dokar ta ɓacin da Bola Tinubu ya ƙaƙaba masu.
Atiku ya ce bayan taron da ya halarta na gamayyar ƴan adawa a Abuja, ya tuntuɓi tsohon gwamnan jihar Ribas, Rufus Ada-George kan halin da suke ciki.

Kara karanta wannan
Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi

Asali: UGC
Alhaji Atiku, tsohon ɗan takarar shugaban kasa na PDP, ya bayyana abin da ya faru bayan ya bar ɗakin taron a Abuja, a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku da manyan ƴan adawa sun haɗe kai
Idan baku manta ba tsohon mataimakin shugaban kasa ya halarci taron manema labarai na gamayyar ƴan adawa a cibiyar Shehu Ƴar'adua da ke Abuja.
A jawabin da ya yi, Atiku ya yi watsi da matakin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas.
Atiku, tare da sauran ƴan adawa da suka kunshi tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun ce Tinubu ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga dokar ta-bacin da aka ƙaƙaba a Ribas.
Bayan kammala wannan taro a Abuja, Atiku ya ce ya samu jin ta bakin dattawa da jagororin al'umma a jihar Ribas kan wannan hali da aka jefa su a ciki.

Kara karanta wannan
Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
Abin da Atiku ya yi bayan taron Abuja
Ya ce tsohon gwamna ya shaida masa cewa sun yi taro kan lamarin, kuma sun cimma matsaya kan dokar ta ɓaci, dakatar da Fubara da ƴan Majalisar Dokokin jiha.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa, Atiku Abubakar ya ce:
"Jim kaɗan bayan na bar cibiyar Shehu Yar’Adua, inda muka yi taron manema labarai tare da hadakar jam’iyyun adawa domin kira ga Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-baci a jihar Rivers, na yi magana da tsohon gwamnan jihar, Cif Rufus Ada-George.
"A lokacin da muka yi magana, Ada-George ya na jagorantar taron dattawan jihar Rivers. Na jaddada masa muhimmancin su tuntubi ‘yan majalisar yankin domin su kada kuri’a kan janye dokar ta-baci a jihar Ribas."
Dattawan jihar Ribas su yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa dattawa da shugabannin Ribas sun yi fatali tare da nuna adawa da dokar ta-baci da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a ayyana a jihar.
Dattawan sun kuma ambaci wasu kalaman da Nyesom Wike ya yi a wata hira da manema labarai, suka ce ya yi kalaman tashin hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng