Tinubu Ya Jawo wa Kansa, Dattawan Ribas Sun Faɗi Matsayarsu kan Dakatar da Gwamna

Tinubu Ya Jawo wa Kansa, Dattawan Ribas Sun Faɗi Matsayarsu kan Dakatar da Gwamna

  • Dattawa da shugabanni a jihar Ribas sun yi Allah wadai da dakatar da Simi Fubara da ƴan majalisa ba tare da dakatar da Nyesom Wike ba
  • Shugaban ƙungiyar dattawan, Rufus Ada-George ya ce idan har Fubara ya yi laifin da za a dakatar da shi, to shi ma Wike ya aikata laifin
  • Dattawan sun kuma yi watsi da ayyana dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi, wanda ya ba da damar tsaida gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Kungiyar dattawan da shugabannin Ribas ta bayyana adawarta da dokar ta-baci da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a ayyana a jihar.

Kungiyar dattawan ta ce matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka babu adalci a cikinsa kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasa.

Wike, Tinubu da Fubara.
Kungiyar manyan jihar Rivers ta yi Allah wadai da dokar ta-baci Hoto: @GovWike, @OfficialABAT, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar, Rufus Ada-George, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis da yake gabatar da matsayarsu kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Channels tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ƴan Majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon watanni shida.

'Shugaba Bola Tinubu ya yi rashin adalci'

Kungiyar ta zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin hukunci na rashin adalci ta hanyar dakatar da Gwamna Fubara da ‘yan majalisa ba tare da daukar wani mataki kan Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.

A cewar dattawan, Wike yana da hannu wajen ruruta rikicin siyasar da ya kai ga ayyana dokar ta ɓaci a Ribas.

"Idan har za a dakatar da Gwamna Fubara da ‘yan majalisar jihar, to dole ne a dauki irin wannan mataki kan Minista Nyesom Wike domin adalci ya tabbata," in ji dattawan.

Dattawan Ribas sun yi fatali da ikirarin Tinubu

Kungiyar ta bayyana cewa Gwamna Fubara ya yi yunkuri sau da dama wajen gabatar da kasafin kuɗin jihar, amma ‘yan majalisa suka hana shi.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

"Don haka, bayyana shi a matsayin wanda bai yi biyayya ba, kamar yadda Shugaba Tinubu ya yi, ba gaskiya ba ne."

- in ji kungiyar dattawan Ribas.

Dattawan sun kuma ambaci wasu kalaman da Wike ya yi a wata hira da manema labarai, inda suka ce ya yi kalaman tashin hankali ta hanyar ambaton yiwuwar lalata bututun mai.

Sun bayyana hakan a matsayin wata dabara da ke nufin jefa jihar cikin rudani don neman dalilin shigar da gwamnatin tarayya cikin rikicin.

Fubara, Tinubu da Wike.
Dattawan Ribas sun bukaci Shugaba Tinubu ya dakatar da Wike Hoto: @SimFubaraKSC, @GovWike
Asali: Facebook

Dattawa sun bukaci a dakatar da Wike

A bisa haka, kungiyar ta bukaci a dakatar da Wike na tsawon watanni shida kamar yadda aka yi wa Gwamna Simi Fubara da ‘yan majalisar jihar.

Dattawan sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci cewa abin da ke faruwa a Jihar Rivers na iya zama barazana ga sauran sassan ƙasa nan gaba.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da bin doka da ida a jihar Ribas

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martanin barazanar dakatar da shi kamar yadda aka yi a Ribas

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da dojar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Ribas.

Majalisar ta yi amfani ne da ikon da take da shi ƙarƙashin tanadin kundin tsarin mulki na shekarar 1999 wajen amincewa da buƙatar shugaban ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng