Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki kan Dokar Ta Bacin da Tinubu Ya Sa a Rivers

Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki kan Dokar Ta Bacin da Tinubu Ya Sa a Rivers

  • Majalisar dattawan Najeriya ta yi muhawara kan buƙatar da Bola Tinubu ya gabatar mata kan dokar ta ɓacin da ya sa a Rivers
  • Bayan gabatar da buƙatar, majalisar dattawan ta amince da matakin da shugaba Tinubu ya ɗauka na sa dokar ta ɓaci a jihar Rivers
  • Majalisar dattawan ta kuma kafa wani kwamitin haɗin gwiwa na musamman da zai kula da harkokin mulki a jihar mai arziƙin mai
  • Za a kuma samar da wani kwamiti da ya ƙunshi manyan ƴan Najeriya domin nemo hanyoyin da za a warware rikicin siyasar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta kaɗa ƙuri'a kan dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Majalisar dattawan ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio, ta amince da dokar ta ɓacin wacce aka sanya a jihar Rivers mai arziƙin mai.

Kara karanta wannan

Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi

Majalisar dattawa ta amince da dokar ta baci a Rivers
Majalisar dattawa ta amince da dokar ta baci a jihar Rivers Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa majalisar ta amince da dokar ta ɓacin ne yayin zamanta na ranar Alhamis, 20 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu

Majalisar dattawan ta yi amfani ne da ikon da take da shi ƙarƙashin tanadin kundin tsarin mulki na shekarar 1999 wajen amincewa da buƙatar shugaban ƙasan ta sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Bayan da Godswill Akpabio, ya karanta bukatar da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa kan dokar ta ɓacin, sai sanatocin suka shiga zaman sirri.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudirin yin zaman sirri bisa tanadin dokar majalisa ta 135, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Abba Moro, ya goyi bayan ƙudirin.

Bayan kammala zaman sirri, Akpabio ya gabatar da batun domin ƙada ƙuri’ar ta hanyar amfani da murya, inda mafi rinjaye suka amince da shi.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Atiku ya tabbatar da shirin kawar da Tinubu a 2027

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa majalisar ta yi amfani da ikon da ta ke da shi bisa sashe na 305(2) na kundin tsarin mulki domin amincewa da buƙatar da shugaban ƙasa ya gabatar.

Amincewar ta ba shugaba Tinubu damar ɗaukar matakan gaggawa, tare da ba da damar sake duba yanayin da ake ciki a kowane lokaci, amma ka da ya wuce watanni shida.

Majalisar dattawa ta ɗauki wasu matakai

Bisa ga tanandin kundin tsarin mulki, majalisar tarayya ta kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin majalisun biyu.

Kwamitin haɗin gwiwar zai riƙa kula da harkokin mulki a jihar Rivers a lokacin da dokar ta ɓacin za ta yi aiki.

Hakazalika, majalisar dattawa ta amince da kafa kwamitin yin sulhu wanda ya ƙunshi manyan ƴan Najeriya domin taimakawa a warware rikicin siyasar jihar Rivers.

Tinubu ya fuskanci bazarana a majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman goyon bayan majalisa domin amincewa da dokar ta ɓacin da ya sanya a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Kiranye daga majalisa: Sanata Natasha ta fadi aɓin da take tsoro

Sai dai, inda gizo ke saƙar ita ce, masu goyon bayan Tinubu na fuskantar turjiya wajen samun haɗin kan sauran ƴan majalisa domin amincewa da dokar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng