2027: Peter Obi Ya Bi Sahun Nasir El Rufai, Mutane Sun Masa Rubdugu a TikTok
- Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi ya buɗe shafi a TikTok yau Talata, 18 ga watan Maris 2025
- Awanni bayan buɗe shafin, Peter Obi ya samu mabiya sama da 6,000, ya kuma bukaci magoya bayansa su bibiye shi a shafin na TikTok
- Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya buɗe shafin TikTok, ya samu mabiya sama da 300,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa karƙashin inuwar jam'iyyar LP, Mista Peter Obi ya buɗe shafi a manhajar sada zumunta ta TikTok yau Talata.
Peter Obi, ya bude shafin kansa na TikTok a hukumance domin kara kusanci da magoya bayansa da kuma yada manufofinsa na siyasa.

Source: Facebook
Peter Obi ya wallafa faifan bidiyo a Tik Tok

Kara karanta wannan
'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai
A wani bidiyo da ya wallafa a shafin na sa a ranar Talata, tsohon gwamnan Anambra ya tabbatar da cewa wannan ne shafinsa na kansa kuma shi kadai gare shi a TikTok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wannan shi ne shafina na kaina kuma shi kadai gare ni a TikTok. Ku zo mu haɗu domin gina sabuwar Najeriya da kowa zai yi alfahari da ita," in ji Obi a cikin bidiyon.
Obi ya samu dubban mabiya a TikTok
Bayan sa’a guda da sanar da bude shafin TikTok din, Peter Obi ya samu mabiya fiye da 6,000.
Haka nan kuma domin saukaka wa masu son bibiyarsa, tsohon gwamnan ya wallafa hanyar zuwa shafinsa a sauran shafukansa na sada zumunta kamar Facebook da X.
Bude shafin TikTok na Peter Obi na zuwa ne kwanaki kadan bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bude nasa shafin a dandalin.
El-Rufai ya riga Obi shiga TikTok
A cikin kwana biyar kacal, shafin El-Rufai ya samu mabiya sama da 323,000, sannan kuma sama da mutum miliyan uku sun duba shafinsa El-Rufai.
Ana ganin manyan ƴan siyasar sun ɗauki wannan matakin ne yayin da suke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Malam El-Rufai a jam'iyyar SDP
El-Rufai ya bude sabon shafin TikTok ne bayan da ya alamta fita daga jam'iyyar APC tare da shiga jam'iyyar SDP mai tambarin doki.
Kasancewar TikTok manhaja ce da ake yada bidiyo, ana kyautata zaton El-Rufai zai ci gaba da yada manufofinsa na siyasa ne da kuma adawa a manhajar mai farin jini wajen matasa.
Zuwansa manhajar ne watakila ya jawo tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi zuwa don tallata manufofinsa.
Hakazalika, akwai yiwuwar a kara samun dandazon 'yan siyasar da za su tattara zuwa TikTok, kasancewar an fi samun matasa maza da mata a can, wanda ka iya sauraran manufofin 'yan siyasa.

Source: Twitter
Obi dai ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023, amma bai samu nasara ba, inda ya zo na uku a jerin ’yan takarar 18 da suka gwabza a zaben.
Jam’iyyar APC da ɗan takararta, shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu ne suka lashe zaben.
Obi na shirye-shiryen zaɓen 2027
Obi, ɗan shekaru 63, wanda ya yi gwamna daga 2007 zuwa 2014 a Anambra, na ci gaba da jan hankalin matasa da ƴan Najeriya ta hanyoyin sada zumunta.
Tsohon gwamnan yana kokarin yaɗa ra’ayinsa na gina "sabuwar Najeriya" da manufofinsa na adalci, kawo ci gaba, da gaskiya a harkokin mulki.
Sai dai, a zaben 2023, bai samu nasarar lashe zabe ba, inda Bola Ahmed Tinubu ya zo na farko tare da Atiku Abubakar a matsayin na biyu sai shi Obi a layi na uku a zaben.
Matasan N/Delta sun goyi bayan Obi da Bala
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar matasa ta yankin Neja Delta (NDYC) ta bayyana goyon bayanta ga shirin hadin gwiwar Gwamna Bala Mohammed da Peter Obi.
Kungiyar ta bayyana cewa haɗin kai tsakanin wadan nan shugabanni biyu alama ce cewa lokaci ya yi na gyara a harkokin siyasar ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar hasashen dalilin zuwan 'yan siyasa manhajar TikTok.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


