Bayan Kama Murja Kunya, Bobrisky Ya Yi Magana kan Sanatoci da Ministoci
- Fitaccen dan daudu a Najeriya da ake kira da Bobrisky ya ce ya taɓa yin soyayya da shahararrun mutane bakwai a Najeriya
- Bobrisky ya bayyana cewa yana shirin fitar da sunayensu a nan gaba kadan, kuma ya ce ya bar Najeriya gaba ɗaya kenan
- Dan daudun ya yi magana ne 'yan sa'ao'i bayan jami'an hukuma mai yaki da rashawa ta EFCC ta cafke 'yar Tiktok, Murja Kunya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shahararren mai shigar mata, Bobrisky ya ce ya taɓa yin soyayya da fitattun mutane bakwai a Najeriya.
Dan daudun ya bayyana cewa yana shirin bayyana sunayensu a nan gaba domin tonawa wasu maƙaryata asiri.

Asali: Instagram
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Bobrisky ya ce ya bar Najeriya gaba ɗaya saboda yadda ake yi masa kallon banza da cin mutunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bobrisky zai bayyana wadanda suka yi soyayya
Bobrisky ya bayyana cewa yana da jerin sunayen fitattun mutanen da ya taɓa yin soyayya da su a Najeriya.
Ya ce lokaci na zuwa da zai fallasa su, domin a cewarsa, akwai mutanen da ke nuna a zahiri su na kirki ne amma suna badala a boye.
A cewarsa, waɗannan shahararrun mutanen suna da fuska biyu; a fili suna nunawa jama’a abu guda, amma a bayan fage suna yin wani abu daban.
Bobrisky ya ce yana jiran lokacin da zai bayyana abubuwan da suka faru tsakaninsa da waɗannan shahararrun mutane.
Me ya sa Bobrisky ya bar Najeriya?
Bobrisky ya ce ba zai dawo Najeriya ba, domin ya samu wata ƙasa da ke mutunta shi a matsayinsa na 'mace.'

Kara karanta wannan
"An takura wa shugaban kasa" Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa daga sukar 'yan adawa
Dan daudun ya ce a sabuwar ƙasar da yake, an amince da shi a matsayin mace kuma ana daraja shi yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa a Najeriya ana yi masa cin mutunci har da manyan jami’an gwamnati kamar ministoci da sanatoci.
Bobrisky ya ce:
“A wane dalili zan bar ƙasar da ake mutunta ni, na je wata ƙasa da ake zagi na da cin mutunci na?”
Bobrisky ya caccaki ministoci da sanatoci
Bobrisky ya ce har yanzu yana mamakin yadda ministoci da ‘yan siyasa ke magana kan lamuransa maimakon su mai da hankali kan ayyukansu.
Dan daudun ya ce:
“Na fahimci cewa ina da muhimmanci sosai tun a watan Nuwamba 2024, lokacin da ministoci da sanatoci suka fara tattauna batu na.”
Ya yi ikirarin cewa idan har zai zauna a Najeriya har tsawon shekaru 100, ba za a taɓa saka “mace” a takardunsa kamar fasfo da lasisin tuƙi ba.
A cewarsa, Najeriya ba wajen zamansa ba ne, kuma ba zai ƙara rayuwa a cikinta ba, illa idan yana buƙatar yin ziyara kawai.

Asali: Instagram
Bobrisky ya ce ba ya tsoron Donald Trump
A wani rahoton, kun ji cewa dan daudun da ya tsere daga Najeriya ya ce baya jin tsoron dokar jinsi da shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya.
Dan daudun ya ce ko da za a bukaci ya nuna cewa shi mace ce a kasar Amurka, to a shirye yake ya tabbatar wa hukumomi hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng