CAN Ta Yabawa Uba Sani, Ta Fadi Yadda Ya Yi Wa Sauran Gwamnoni Zarra

CAN Ta Yabawa Uba Sani, Ta Fadi Yadda Ya Yi Wa Sauran Gwamnoni Zarra

  • Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna na jin daɗin salon mulki irin na mai girma Gwamna Uba Sani
  • Shugaban CAN na Kaduna, Fasto Caleb Ma'aji ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yi wa gwamnan addu'ar
  • Ya yabawa Gwamna Uba Sani kan yadda yake jawo Kiristoci a jiki domin su ba da ta su gudunmawar wajen ci gaban jihar
  • Fasto Caleb Ma'aji ya nuna cewa a bayyane yake a fili cewa gwamnatin Uba Sani ta fi wacce ta gabace ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, Fasto Caleb Ma’aji, ya yaba da salon mulkin Gwamna Uba Sani.

Fasto Caleb Ma'aji ya bayyana cewa Kiristoci za su ci gaba da yi wa Gwamna Uba Sani addu’a domin samun nasara, kasancewar yana damawa da su.

Kara karanta wannan

'Gwanda Buhari': Shugaban jam'iyya ya fadi azabar da ake sha a mulkin Tinubu

CAN ta goyi bayan Uba Sani
CAN ta ce za ta ci gaba da yi wa Uba Sani addu'a Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Shugaban na CAN ya bayyana hakan ne a lokacin liyafar buɗa baki da Gwamna Uba Sani ya shiryawa limaman coci da manyan shugabannin Kiristoci a gidan gwamnati a ranar Lahadi, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar CAN ta yabi Uba Sani

Fasto Caleb Ma’aji ya yabawa gwamnan bisa manufofinsa na haɗa kan kowa da kowa a jihar, wanda ke ba dukkan ɓangarori damar taka rawarsu wajen ci gaban Kaduna.

Shugaban na ƙungiyar CAN ya bayyana bambancin gwamnatin Uba Sani da ta baya a bayyane yake.

A cewarsa, salon mulkin Gwamna Uba Sani ya sha bamban da na gwamnatocin da suka gabata, kuma hakan ya ba Kiristoci a jihar Kaduna ƙwarin gwiwar jin cewa su ma ƴan jihar ne.

"Shugabancinka ya zama jigon addu’o’inmu. Ba za mu daina yi maka addu’a ba har sai alkhairinka ya na yau yafi na baya, na gobe yafi na yanzu."

Kara karanta wannan

Zargin El Rufai: Gwamna Uba Sani ya yi martani, ya fadi abin da ya sa a gaba

- Fasto Caleb Ma'aji

Uba Sani ya na damawa da Kiristoci

Shugaban CAN ya tuna cewa a shekarar 2023, Gwamna Uba Sani ya halarci taron bikin Kirsimeti a karo na farko a jihar Kaduna, inda ya yi alƙawarin ci gaba da halarta a duk shekara.

"A bara, ya cika alkawarinsa, ya halarci bikin a karo na biyu. Ya nuna mana soyayya, har ma ya tallafa mana. Muna matukar godiya."

- Fasto Caleb Ma'aji

Shugaban na CAN ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani har ma ya yi alkawarin cewa taron bikin Kirsimeti na shekara mai zuwa zai zama nasa, domin yana son ya ci abinci tare da mutanensa kuma ya sha Fanta da su.

Gwanna Uba ya maida hankali kan mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa bai da lokacin ɓatawa wajen yin ƴan ƙananan maganganu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa babban ƙudirinsa shi ne ya ga ya gudanar da mulkin jihar Kaduna yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Madalla da hutu ga yan sakandare domin azumin watan Ramadan

Uba Sani ya nuna cewa yana da ƙudirin ganin ya sauke nauyin da mutane suka ɗora masa na shugabancin jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel