Kaduna: 'Yan Kasuwa Sun Yi Zanga Zanga, Sun Tuna da Yadda El Rufa'i Ya Jawo Masu Matsala
- Daruruwan ‘yan kasuwa a Kaduna sun gudanar da zanga-zanga domin tunawa da rushe wuraren kasuwancinsu a mulkin Nasir El-Rufa’i
- Zanga-zangar ta gudana a gaban Kasuwar Malam Sheikh Abubakar Muhammed Gumi, ‘yan kasuwa suka nuna damuwarsu kan batun
- Sun kara da shawartar jama'ar Kaduna kan matsalar da za su fada, matukar su ka sake goyon bayan tafiyar siyasar da El-Rufa'i ya dauko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Daruruwan mata da ‘yan kasuwa a Kaduna sun gudanar da zanga-zanga domin tunawa da rushe kasuwanni da wuraren kasuwanci a lokacin mulkin tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i. Zanga-zangar ta gudana a gaban Kasuwar Malam Sheikh Abubakar Muhammed Gumi, inda ‘yan kasuwar da abin ya shafa suka hallara domin nuna damuwarsu kan halin da aka jefa su a ciki.

Kara karanta wannan
El Rufai ya gamu da matsala bayan komawa SDP, ƴan kasuwa da mata sun yi masa bore

Asali: Facebook
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa wadannan ‘yan kasuwa sun rasa kasuwanninsu da wuraren sana’o’insu sakamakon rushewar da aka yi a jihar.
'Yan kasuwa sun goyi bayan gwamna Uba Sani
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yayin da ake fuskantar zaben 2027, ‘yan kasuwar sun sake tabbatar da biyayyarsu ga gwamnatin gwamna Uba Sani da kuma Shugaba Bola Tinubu. Masu zanga-zangar, wadanda suka fito daga sassa daban-daban na jihar Kaduna, sun bayyana cewa sun sha wuya a lokacin mulkin Nasir El-Rufa’i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Facebook
Sun zargi tsohuwar gwamnatin da amfani da dokoki masu tsauri wajen danniya da tauye hakkin al’ummar jihar, kuma ta hana su samun abin dogaro da kai. Sun sha alwashin tsayawa tsayin daka tare da gwamna Sani, inda suka gargadi jama’ar Kaduna da kada su bari a ja su zuwa wata jam’iyya ko akidar siyasa daban.
‘Yan kasuwa sun yi tir da El-Rufa'i
Wani daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa, Malam Sumaila Ilya, ya bayyana cewa babu wata dabarar siyasa da za ta iya wanke halayen tsohon gwamna El-Rufa’i. A yayin zanga-zangar, ‘yan kasuwar sun bukaci al’umma da su yi watsi da duk wata aniyar siyasa da El-Rufa’i zai yi a nan gaba, inda suka sha alwashin cewa ba za su goyi bayansa ba. ‘Yan kasuwar da suka fusata saboda abin da suka kira “rushewa ba bisa ka’ida ba,” sun nuna cikakken goyon bayansu ga jagorancin gwamna mai ci, Sanata Uba Sani.
Gwamna Uba ya yi martani ga El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada cewa burinsa na yin hidima ga jama'ar jihar Kaduna da suka zabe shi, maimakon ya riƙa biyewa maganganu marasa amfani.
Gwamna Uba Sani ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ake ce-ce-ku-cen sauya shekar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi zuwa SDP a shirin kayar da Tinubu a zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng