"Gwamnatin Najeriya na Shirin Kama Ni": Sanata Natasha Ta Fadi Halin da Take Ciki
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ana shirin cafke ta idan ta dawo Najeriya saboda halartar taron IPU da aka gudanar a Amrurka
- Hukumomin sirri na DSS da NIA suna binciken yadda ta samu damar halartar taron ba tare da izini ba, da wanda ya taimaka mata a tafiyar
- Sanatar ta yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya tura jami’ai don korar ta daga harabar Majalisar Dinkin Duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zargin cewa jami’an tsaron Najeriya na shirin cafke ta da zarar ta dawo gida daga Amurka.
Ta danganta shirin kama ta da halartar taron kungiyar 'yan majalisu na duniya (IPU) da aka gudanar a New York a ranar 11 ga Maris.

Asali: Twitter
"Ana shirin kama ni" - Sanata Natasha

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
A wajen taron, ta bayyana damuwarta kan dakatarwar da aka yi mata daga majalisar dattawa da kuma zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban Majalisa, Godswill Akpabio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da jaridar Premium Times ta wayar tarho a ranar Lahadi, 16 ga watan Maris.
“Na samu labari cewa ana shirin cafke ni da zarar na iso Abuja,” in ji Akpoti-Uduaghan, wadda har yanzu tana Amurka bayan ta halarci taron IPU.
Sai dai rahoton jaridar ya nuna cewar 'yan majalisar dattawan ba ta bayyana wacce hukuma ce ke shirin kama ta ba.
DSS, NIA sun fara bincike kan Sanata Natasha
A baya, mun ruwaito cewa hukumomin sirri na cikin gida da na waje sun fara bincike kan yadda Sanata Natasha ta samu damar halartar taron IPU ba tare da izini ba.
Wata majiya daga gwamnati da jami’an tsaro biyu da ke da alaka da binciken sun tabbatar da cewa DSS da NIA na kokarin gano yadda ta samu damar shiga taron.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jami'an EFCC sun cafke fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya a Kano
Hukumomin sun ce suna binciken wanda ya taimaka mata, da kuma ko wasu ƙungiyoyi ne suka shirya tafiyarta don bata wa Najeriya suna a taron.
"Akpabio ya turo a kore ni daga IPU" - Natasha

Asali: Facebook
Sanata Natasha dai ta yi zargin cewa bayan jawabin da ta yi a taron, Sanata Akpabio ya tura jami’an diflomasiyya uku daga ofishin jakadancin Najeriya a New York don korar ta daga wajen taron.
“Shugaban majalisa Akpabio ya tura jami’ai uku karkashin shugaban harkokin ofishin jakadancin Najeriya a New York don fitar da ni daga harabar Majalisar Dinkin Duniya."
- Sanata Natasha.
Ta ce sai da ’yan majalisar dokoki daga wasu ƙasashe da jami’an tsaro suka hana a kore ta daga wajen taron.
An yi kokarin jin ta bakin shugaban majalisar dattawa Akpabio, amma bai amsa kiran waya ko sakon kar-ta-kwana da aka aike masa ba.
Haka nan, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun majalisar dattawa, Yemi Adaramodu ba, domin layin wayarsa bai shiga ba.

Kara karanta wannan
Sanata Natasha ta shiga matsala, DSS, NIA sun fara bincikar ta kan zuwa taron IPU
Har yanzu ba a samu wata sanarwa daga hukumomin Najeriya ko majalisar dattawa kan shirin kama Akpoti-Uduaghan ko zargin da take yi ba.
SERAP ta maka Sanata Akpabio a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, SERAP ta gurfanar da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a kotu kan dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
An shigar da ƙarar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda SERAP ke neman a soke dakatarwar wata shida da aka yi wa sanatar bisa tauye hakkinta.
Asali: Legit.ng