Wata Sabuwa: Jami'an EFCC Sun Cafke Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya a Kano

Wata Sabuwa: Jami'an EFCC Sun Cafke Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya a Kano

  • Hukumar EFCC ta kama shahararriyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, a Kano bisa zargin bata martabar Naira a waje wani biki
  • Wata majiya daga EFCC ta ce an kama Murja kwanaki uku da suka gabata, kuma idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu
  • An ruwaito cewa Murja Kunya ta tsere daga beli a baya, amma an sake cafkarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan irin laifin da ta yi
  • Kama ta ya janyo martanin jama’a, inda wasu ke ganin hakan darasi ne ga wadanda suka shahara a intanet, don gujewa fushin hukuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa hukumar EFCC reshen jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar TikTok ta Arewa, watau Murja Ibrahim Kunya.

An tabbatar da cewa hukumar da ke yaki da rashawa da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa, ta cafke Murja Kunya bisa zargin bata martabar takardar Naira.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Najeriya na shirin kama ni": Sanata Natasha ta fadi halin da take ciki

EFCC ta cafke Murja Kunya a Kano
Ana zargin EFCC ta cafke Murja Kunya kan wulakanta takardar Naira. Hoto: Murja Ibrahim Kunya, EFCC
Asali: Facebook

EFCC ta cafke Murja Ibrahim Kunya

Wata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, inji rahoton Freedom Radio Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.

Rahotanni sun nuna cewa an kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta jiya.

Sharar Murja Kunya da shigarta komar EFCC

Murja Kunya ta fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin sha'awa kawai, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a.

A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kanta.

Express Radio Kano ya rahoto cewa EFCC ta kama Murja daga cikin matakan hana mutane wulakanta Naira a wuraren taruka da bukukuwa, kamar yadda aka sha ganin tana yi.

Kara karanta wannan

Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

To sai dai har zuwa yanzu, hukumar EFCC ko lauyoyin Murja Kunya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan lamari ba.

Yayin da majiya daga hukumar ta ce ana ci gaba da bincike, mutane suna zaman jira, domin samun karin bayani kan lokacin fara shari'ar Murja Kunya.

Kama Murja gargadi ne ga masu wulakanta Nair

Ana zargin EFCC ta cafke Murja Ibrahim Kunya a Kano
Rahotanni sun nuna cewa Murja Ibrahim Kunya ta shiga hannun hukumar EFCC. Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: Instagram

Wannan lamari ya haddasa muhawara kan rawar da masu tasiri a kafafen sada zumunta ke takawa wajen bin doka ko akasin haka.

Ko a baya, hukumar EFCC ta yi kira ga jama’a da su kiyaye dokokin Najeriya, musamman dangane da yadda ake wulakanta Naira a wajen bukukuwa.

Kama Murja Kunya na iya zama izina ga wadanda suka shahara a kafafen sada zumunta, don gujewa abubuwan da ka iya jawo fushin hukuma a kansu.

EFCC ta cafke mai shigar mata, Bobrisky

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar EFCC ta kama fitaccen ɗan daudu, Idris Okuneye (Bobrisky), bisa zargin watsa takardun naira da cin mutuncin kudin Najeriya,

An kama Bobrisky a Legas, inda aka tsare shi a ofishin EFCC yayin da hukumar ke ci gaba da gudanar da bincike kan karya dokar kasar da ya yi na mutunta Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel