Wata Sabuwa: Rahoto Ya Gano Najeriya Ta Fi Saudiyya Kashe Kudi Wajen Hako Danyen Mai
- Rahoto ya gano cewa, Najeriya na daga kasashen da suka fi kowacce kasa kashe kudi wajen hako danyen mai a duniya
- Kasar Saudiyya ta fi Najeriya samun sauki wajen kashe kudin hako danyen man fetur idan aka kwatanta kudin da suke kashewa
- NUPRC ta ce wannan babbar barazana ce ga tattalin arzikin Najeriya, kuma akwai bukatar tabbatar da an sauya hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Najeriya - Rahoton Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya nuna cewa kudin da ake kashewa wajen hakar danyen mai a Najeriya ya karu zuwa kusan dala 40 a kowace ganga.
A cewar jaridar The Punch, wannan farashi ya ninka sau uku idan aka kwatanta da dala 10 da ake kashewa domin hakar ganga daya a kasar Saudiyya.
Hukumar NUPRC ta nuna damuwa cewa wannan matsala na iya kara sanya Najeriya cikin wahalar yin gogayya a kasuwar duniya sakamakon hauhawar farashin hakar danyen mai da kuma sauyin farashin mai a duniya.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

Asali: Getty Images
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wani rahoto, NUPRC ta bayyana cewa:
"A takaice, ana kashe tsakanin dala 25 zuwa 40 wajen hakar ganga daya ta danyen mai a Najeriya, wanda ke daga cikin mafi tsada a duniya.
"Wannan farashi yana da matukar nisa idan aka kwatanta da kasashe masu arzikin mai irin su Saudiyya, inda fasaharsu ta inganta matuka har suke kashe kasa da dala 10 a kowace ganga."
Farashin danyen mai a kasuwar duniya
Hukumar ta bayyana cewa, idan farashin mai a duniya ya tsaya a dala 75 kowace ganga, hakan na nufin masana'antun mai a Najeriya za su riga kashe rabin wannan kudi wajen hakowa kawai.
Ta kuma bayyana cewa akwai matsaloli da dama da ke haddasa tsadar hakar mai a kasar, ciki har da tsofaffin bututun mai da wuraren ajiya da ke bukatar gyara akai-akai.
Hukumar ta ce ana bukatar sabunta wadannan kayayyakin aikin domin rage kudin gyara, tsawaita jimawarsu suna aiki da kara inganta samar da danyen mai.
A cewar hukumar:
"Satar mai da lalata bututun mai su ne manyan matsalolin da ke janyo tsadar aiki a bangaren. Najeriya na sane da wannan matsala, kuma tana daukar matakai don magance su.
"Dokar Masana’antar Man Fetur da aka kafa a shekarar 2021 na daya daga cikin muhimman matakan da aka dauka domin shawo kan wadannan matsaloli."
Kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi
NUPRC ta bayyana cewa ana kokarin rage kudin hakar danyen mai zuwa dala 20 a kowace ganga.
NUPRC ta kara da cewa:
"Tun bayan kafa NUPRC a matsayin hukumar da ke da alhakin kula da bangaren hakar danyen mai, ta dauki matakai don shawo kan wadannan matsaloli. A shekarar 2023, bayan shekaru biyu da kafuwarta, hukumar ta fitar da wani shiri na tsawon shekaru goma domin farfado da bangaren hakar mai.
"A cikin shekarar 2024, a wani shirin gajeren zango na tsare-tsaren da aka kaddamar, hukumar ta fitar da wani shirin aiki mai mahimmanci da daya daga cikin manyan burinta shine rage kudin hakar danyen mai zuwa akalla dala 20 a kowace ganga."

Kara karanta wannan
Albashi N500,000: 'Yan kasar Sin suka shigo Najeriya, sun kafa kamfanin sarrafa lithium a Nasarawa
Gargadi ga wasu kamfanonin mai
Hukumar ta yi gargadi cewa kamfanonin da ba su mai da hankali kan rage kudin hako ba, za su ci gaba da fuskantar kalubale wajen janyo masu zuba jari, samun riba mai yawa da kuma dorewar kasuwancinsu a cikin matsin tattalin arziki.
Rahoton ya kara da cewa, tun da man fetur ke da kaso 90% na kudin shiga daga harkokin kasuwanci na Najeriya kuma babbar hanyar samun kudin shiga ga gwamnati, tsadar hakar mai na iya yin barazana ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, duk da cewa akwai manyan kalubale a gaban Najeriya wajen cimma wannan buri, amfanin rage kudin hakar mai zai fi kowanne tasiri ga ci gaban tattalin arziki.
Babban abin da ya kamata a mai da hankali
Ta kuma kara da cewa:
"Idan aka rage farashin hakar mai, hakan zai kara janyo hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya, wanda zai baiwa kasar damar yin gogayya da sauran kasashe masu arzikin mai da kuma tabbatar da matsayin ta a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan
Ana fargabar gwamnatin Trump za ta kori 'yan Najeriya da ke karatu a kasar Amurka
"Karin ribar da hakan zai haifar zai amfani kamfanonin mai da masana’antu, kuma hakan na iya haifar da karuwar haraji da kudin haya da za su kara bunkasa ajiyar kudaden Najeriya da kuma karfafa tattalin arzikinta a kasuwar duniya."
Dangote ya sayo dnayen mai daga kasar waje
A wani labarin, kun ji yadda Dangote ya tsallaka Najeriya ya fita kasar waje domin saye danyen man fetur.
Wannan ya faru ne sakamakon rashin samun wadataccen danyen mai da zai iya tacewa da ake hakowa a kasar.
Tun kafa matatar man Dangote ake kai ruwa rana da shi, inda ake zargin yana kokarin mamaye kasuwar harkar man fetur.
Asali: Legit.ng