Sanata Natasha Ta Shiga Matsala, DSS, NIA Sun Fara Bincikar Ta kan zuwa Taron IPU

Sanata Natasha Ta Shiga Matsala, DSS, NIA Sun Fara Bincikar Ta kan zuwa Taron IPU

  • Gwamnatin Tarayya na bincike kan yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci taron kungiyar IPU ba tare da sahalewar Najeriya ba
  • DSS da NIA na binciken ko an shirya halartar nata don cin zarafin gwamnati, ko kuma ta karya dokokin IPU da na majalisar dokokin kasar nan
  • Sanata Natasha ta yi zargin cewa an dakatar da ita ne don hana ta bayyana wasu laifuffuka, amma majalisa ta ce an dakatar da ita kan saba dokoki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara bincike kan yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta halarci taron Kungiyar Majalisun Duniya (IPU) ba tare da sahalewar Najeriya ba.

Rahoto ya bayyana cewa manyan hukumomin tsaron Najeriya, DSS da NIA ne ke gudanar da binciken don gano wanda ya ba sanatar damar shiga taron.

Kara karanta wannan

An karrama Buhari tare da manyan malamai da 'yan siyasar Najeriya

Gwamnatin tarayya ta fara bincikar Sanata Natasha kan halartar taron kungiyar IPU
Halartar taron IPU ya jefa Sanata Natasha a matsala, gwamnati ta fara bincike. Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Ana zargin Natasha ta karya doka a zuwa IPU

Binciken zai tantance ko an shirya halartar nata don cin zarafin gwamnatin Najeriya, da kuma ko ta karya dokokin IPU ko na majalisar dokokin kasar, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IPU kungiya ce ta ‘yan majalisar dokoki ta duniya da ke da ka’idojin da ke bukatar duk wanda zai wakilci kasa ya sami amincewa daga hukumomin kasarsa.

Najeriya na tura zababbun ‘yan majalisar dattawa da na wakilai tare da jami’an majalisa, kuma dole ne a amince da duk wanda zai halarci zaman kungiyar a matsayin dan-sa-ido.

Amma hukumomin Najeriya sun ce Sanata Akpoti-Uduaghan ba ta bi ka’idojin da ake bukata kafin ta shiga taron IPU da aka gudanar a ranar 11 ga Maris ba.

Majalisa ta kalubalanci Natasha kan zuwa IPU

A wajen taron, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha ta yi jawabi kan dakatarwarta daga majalisar dattawa, tana mai cewa an yi hakan ne don hana ta bayyana wasu laifuka.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Ta kuma yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nemi yin lalata da ita, abin da ya tayar da kura a cikin taron.

A martaninta, shugabar IPU, Tulia Ackson, ta ce za a binciki batun tare da bai wa majalisar dattawan Najeriya damar kare kanta.

Sai dai, wata mamba a tawagar Najeriya, Kafilat Ogbara, ta musanta ikirarin Natasha, tana mai karanta wasikar da ke bayyana dalilin dakatarwarta.

A cewar Opeyemi Bamidele, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya ce an dakatar da Natasha ne saboda karya dokokin majalisa, ba wai saboda zarge-zargenta ba.

DSS, NIA sun fara bincikar Natasha kan zuwa IPU

DSS, NIA sun fara bincikar Sanata Natasha
DSS, NIA sun fara bincikar Sanata Natasha. Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Kuma Sanata Bamidele ya ce ‘yan majalisa da aka tantance ne ne kawai za su iya wakiltar Najeriya a tarukan kasa da kasa irin na IPU.

Shi ma Sanata Jimoh Ibrahim ya tabbatar da cewa Natasha ba ta da wata takardar izini daga majalisar dattawa ko kwamitin hulɗa da IPU na halartar taron.

Kara karanta wannan

Natasha: Kungiyar 'yan majalisun duniya ta karbi koken Sanata, za ta ji ta bakin Akpabio

DSS da NIA na binciken ko an ba Sanata Natasha takardun bogi, ko wani ya taimaka mata shiga taron ba tare da izini ba.

Binciken zai kuma gano ko an karya dokokin IPU ko na majalisar Najeriya, da kuma ko wasu kungiyoyi ne suka taimaka mata samun damar halartar taron.

SERAP ta maka Apabio a kotu kan Natasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, SERAP ta yi karar Godswill Akpabio a kotu kan dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

SERAP ta bayyana cewa dakatarwar wata shida ta take haƙƙin sanatar, tare da hana al'ummar Kogi ta Tsakiya damar samun wakilci a majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel