Gobara Kashe Mutane 7, Ta Lalata Kadarorin Naira Miliyan 50 a Jihar Kano

Gobara Kashe Mutane 7, Ta Lalata Kadarorin Naira Miliyan 50 a Jihar Kano

  • Hukumar kashe gobara ta Kano ta ceci mutane 7 da dukiyar Naira miliyan 180 daga gobara 77 da suka faru a cikin watan Fabrairu, 2025
  • Rahotanni a tsakanin wannan lokaci ya nuna cewa gobara ta kashe mutane tare da lalata kadarori da darajarsu ta kai Naira miliyan 50
  • Legit Hausa ta tuno wasu daga cikin gobarar da suka faru, ciki har da gobarar Bunkure da ta kone gidaje, dabbobi da rumbunan hatsi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceto mutane bakwai da kadarorin da suka kai darajar Naira miliyan 180 daga gobara 77 da suka faru a watan Fabrairu.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

Hukumar kashe gobara ta yi magana kan asarar rayukan da aka yi a gobara 77 da suka faru a Kano
Hukumar kashe gobara ta fitar da rahoton gobara 77 da suka afku a Kano a Fabrairun 2025. Hoto: @Fedfireng
Asali: UGC

Gobara ta halaka mutane 7 a Kano

A cewarsa, mutane bakwai sun rasa rayukansu, yayin da gobara ta lalata dukiyar da ta kai darajar Naira miliyan 50 a tsakanin wannan lokaci, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Saminu Abdullahi ya shaida cewa:

"Gobara a watan Fabrairu ta lalata kimanin kadarori na N50,318,000, yayin da kiyasin dukiyoyin da jami’an kwana-kwana suka ceci ya kai N180,318,000.
“Mutane bakwai sun rasa rayukansu sakamakon wadannan gobara, yayin da hukumar kwana-kwana ta ceci mutane bakwai.”

Ya shawarci jama’a da su kula da kayayyakin wutar lantarki a gidaje da shagunansu, ta hanyar kashe kayan lantarki kafin su fita.

Haka kuma, ya bukaci direbobi da su rika yin tuki a hankali, musamman a lokacin bukukuwa domin guje wa hadurran da ba a tsammani.

Wasu daga cikin gobarar da aka yi a Fabrairu

Legit.ng Hausa ta rahoto wasu daga cikin gobarar da aka yi a jihar Kano a watan Farairun 2025:

Kara karanta wannan

An yi amfani da sunan matar gwamnan Katsina, an damfari mutane Naira miliyan 197

Gobara ta babbake dabbobi masu yawa

Akalla shanu, tumaki, awaki da kaji 78 sun kone a wata gobara da ta tashi a kauyen Danzago, karamar hukumar Dambatta a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu a gidan Ado Yubai.

Haka zalika, Saminu ya ce gobarar ta bazu zuwa gidan Ibrahim Mai Gariyo, inda rumfa ɗaya da tumaki takwas da awaki uku suka kone.

Mun ruwaito cewa wani jami'in hukumar kashe gobara ya ji rauni a kafa yayin kokarin kashe gobarar amma an tabbatar da cewa babu asarar rai.

Gobara ta babbake gidaje a Bunkure

Hukumar kwana-kwana ta magantu kan gobarar da ta tashi a Kano Fabrairu
An samu tashin gobara sau 77 a jihar Kano a Fabrairun 2025, inji hukumar kwana-kwana. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wata gobara da ta tashi a kauyen Satigal da ke karamar hukumar Bunkure a jihar Kano ta kone gidaje da dama, dabbobi, da kuma rumbunan ajiyar hatsi guda shida.

Duk da cewa ba a rasa rai ba, gobarar ta jawo asarar kayayyaki da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tabargazar sace sarki da dare, an kama mutum 5

A cewar wata sanarwa daga jami’in yada labarai na yankin Rano, Rabi’u Kura, mazauna yankin sun hada kai wajen kashe gobarar, lamarin da ya hana ta yin barna mai yawa.

Wani rahoton Daily Trust ya nuna cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga Sarkin Rano, Jakadan Kasa, Dakta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa.

Ana zargin cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar girki da aka bari ba tare da kulawa ba daga daya daga cikin gidajen da abin ya shafa.

Yayin da yake nuna juyayi ga wadanda gobarar ta shafa, an ce sarkin ya ba da tallafin N200,000 domin taimaka masu.

Gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da ke Mundubawa a daren Lahadi, 5 ga Mayu, 2024.

Gobarar, wacce ta fara daga ɗakin girki, ta bazu zuwa ɗakin matarsa ta uku, Halima Shekarau, inda ta haddasa lalacewa mai yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel