Arewa Ta Yi Rashi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Rahotanni sun bayyana cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Chief Patrick Adaba, ya rasu a Abuja bayan fama da gajeriyar jinya
- Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana Chief Adaba a matsayin shugaba nagari da ya yi aiki cike da kishin kasa, gaskiya da sadaukarwa ga jiharsa
- Gwamna Ahmed Ododo ya aika da ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana mai cewa za a ci gaba da tunawa da kyawawan ayyukan Chief Adaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Chief Patrick Adaba, ya rasu a ranar Lahadi a Abuja, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Majiyoyi sun bayyana cewa rasuwarsa ta Janar na hukumar kula da sadarwa ta kasa (NBC).

Source: Facebook
Tsohon mataimakin gwamnan Kogi ya rasu
A cikin wata sanarwa, gwamnatin jihar Kogi, ta nuna alhinin rasuwar Chief Adaba, tana mai bayyana shi a matsayin mutum mai dattako, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar da sanarwar rasuwar tsohon mataimakin gwamnan a ranar Litinin.
Kingsley Fanwo ya ce Chief Adaba ya yi aiki da kishin kasa, gaskiya da jajircewa a matsayin mataimakin marigayi Gwamna Abubakar Audu.
"Adaba ya kasance abin koyi" - Gwamnatin Kogi
Ya kara da cewa marigayin ya taka rawar gani wurin kafa tubalin ci gaban jihar Kogi, wanda ba za a taba mantawa da shi ba.
Sanarwar kwamishinan ta ce:
“Ya kasance abin koyi ga shugabannni, la'akari da sadaukarwarsa, wanda ya bayar da gudunmawa wajen bunkasa jihar da kasa baki daya."
Kingsley Fanwo ya ce mutuwar tsohon mataimakin gwamnan ba rashi ne kawai ga iyalansa da kabilar Ebira ba, har ma ga daukacin jihar da Najeriya baki daya.
A cewarsa, za a ci gaba da tunawa da Chief Adaba bisa hidimarsa ga al’umma, kaunarsa ga mutane da kuma kyawawan abubuwan koyi da ya bari.
Gwamnan Kogi ya yi alhinin rasuwar Adaba

Source: Facebook
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan Adaba da daukacin mutanen jihar Kogi bisa wannan babban rashi.
Ododo ya ce marigayin ya yi hidima ga jiharsa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai cewa za a ci gaba da koyon darasi daga rayuwarsa.
Ya kara da cewa Chief Adaba yana da kishin al'ummar Kogi, kuma har bayan barinsa mulki, gwamnati na shawara da shi kan harkokin cigaban jihar.
Tribune ta rahoto gwamnatin Kogi ta bayyana cewa za a yi kewar marigayin, tana mai addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Har ila yau, an roki Allah bai wa iyalansa da duk wadanda rasuwarsa ta shafa hakurin jure wannan babban rashi da suka yi.
Tsohon gwamnan Akwa Ibom ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, al'ummar Akwa Ibom sun shiga jimami bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Manjo-Janar Godwin Osagie Abbe.
An rahoto cewa Janar Godwin Osagie Abbe ya rasu ne a birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar, 21 ga Disamba, 2024, bayan doguwar jinya.
Kafin rasuwarsa, ya shugabanci jihohin Akwa Ibom da Rivers a matsayin gwamnan soja, sannan ya rike mukamin Ministan Najeriya a mulkin marigayi Umaru Musa Yar'Adua.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


