Cibiya ta Binciko Abin da Ya sa Jami'o'in Ketare Suka Yi wa Na Najeriya Nisa

Cibiya ta Binciko Abin da Ya sa Jami'o'in Ketare Suka Yi wa Na Najeriya Nisa

  • Cibiyar Athena ta gudanar da wani bincike a game da yadda ake tafiyar da harkokin wasu manyan jami'o'i a Najeriya
  • Abin da aka gano shi ne akwai boye-boye game da sha'anin kashe kudi kuma babu wani abin a yaba a babin shirya bincike
  • Muddin makaranta ta yi kasa a wajen alkaluman TI da ke nuna gaskiyarta, ba za ta rike samun kudi daga manyan duniya ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Cibiyar Athena da ke bincike wajen harkar tsare-tsare da shugabanci ta fitar da rahoto game da gazawar jami'o'in Najeriya.

Wani bincike mai ban tsoro da aka yi ya nuna babu makarantar Najeriya da duniya ta san yadda kudi su ke shiga su fita cikinta.

Jami'a
An sha gaban jami'o'in da ke Najeriya a duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit Hausa ta karanta sakamakon wannan bincike ta hannun wani jami'in cibiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike game da jami'o'in Najeriya duniya

Dr. Arthur Nwankwo da Farfesa Olikoye Ransom suka gabatar da sakamakon wannan bincike ranar Laraba a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Aikin da Dr. Arthur Nwankwo da Farfesa Olikoye Ransom suka gudanar ya nuna yadda aka binciki manyan makarantu har 64.

A nan aka gano cewa babu wata jami'a da ta iya nunawa yadda ta kashe kudin da ta tatsa duk da cewa an bukaci wannan bayani.

Yadda taron Athena ya samu albarka

Wannan taro da aka yi ya samu halartar Dr. Ejeb A.U a madadin karamin ministan ilmi kamar yadda The Nation ta kawo rahoto.

Irinsu Sanata Dino Melaye da tsohon ministan wasanni, Bolaji Abdullahi da Farfesa Osita Chidoka sun je, har wasu sun yi magana.

Kalubale a gaban jami'o'in Najeriya

Idan aka cigaba da tafiya ta wannan salo na nuku-nuku, za a kora masu ruwa da tsaki da ke sha'awar zuba kudi a harkar ilmi.

Jami'o'in da suke gudanar da ayyukansu a fili ne suke samun kudi daga duniya domin malamai su yi bincike da nazarin ilmi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon hadimin shugaban kasa ya rasu yana da shekaru 72

Akwai bukatar a ga jami'a ta na fito da kirkire-kirkire na zamani kuma ta samu karbuwa daga daliban wasu kasashen waje.

Binciken ya nuna idan aka zo bangaren sanin keke-da-keke da gaskiyar abin da jami'o'i ke batarwa, an bar Najeriya a baya.

Jami'a
Jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit Hausa ta lura cewa makarantun Kenya, Afrika ta Kudu, Masar da Ghana sun yi wa irinsu ABU, OAU da jami'ar Legas nisa.

Daily Trust ta ce duk da dokar FOA ta 2011 da ka'idojin NUC suna aiki, ba a san hakikanin yadda ake tafiyar da jami'o'in ba.

Wajen samun kudi a duniya, ana amfani da alkaluman TI domin sanin gaskiyar jami'a a sha'anin kashe kudi da gudanarwa.

Abubuwan da ake la'akari da su sun hada da nagartar shafin yanar gizo, bayanin batar da kudi, tsarin daukar aiki da raba kwangila.

Haka zalika cibiyar ta ce matakan yaki da rashin gaskiya yana tasiri wajen sanin matsayin makarantun na gaba da sakandare.

Kara karanta wannan

Makusancin Kwankwaso, Buba Galadima ya hango illar saukar farashin abinci

Makarantun da suka ciri tuta a nan suna samun kudi daga kungiyoyin duniya kuma su na shiga yarjejeniya da kasashen ketare.

Jami'o'in Singapore, Pretoriam, Cambridge da Cairo sun samu miliyoyin daloli ta yarjejeniyoyi, gudanar da bincike da sauransu.

Cibiyar Athena ta ba jami'o'i mafita

Idan makarantun kasar suna son a rika damawa da su dole sai an fito da sabon tsarin da zai tabbatar da gaskiya a gudanarwa.

Wajibi ne duniya ta san yadda jam'i'o'in suke batar da kudinsu kuma su ba dama masu binciken kudin gida da waje su bibiya.

Bayan gyara kwamitin da ke sa ido, cibiyar Athena ta ba hukumar wasu shawarwarin inganta gaskiya a idonun duniya.

Sannan dole shugabannin makarantun su rika ba da bayanin kudin da aka samu.

An sace dalibai a jami'ar Najeriya

A can kwanakin baya aka samu rahoto cewa an yi awon gaba da ɗaliban jami'ar tarayya a jihar Taraba lokacin da ake karatu.

Miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da ƴan makarantar ne a ɗakin kwanansu. Jami'an tsaro sun yi azama domin a ceto su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel