Ana cikin Rigima da El Rufai, Gwamna Uba Sani Ya Sha Sabon Alwashi a Kaduna

Ana cikin Rigima da El Rufai, Gwamna Uba Sani Ya Sha Sabon Alwashi a Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana ƙudirin da ya ke da shi kafin ya sauka daga kan mulki a Mayun 2027 ko 2031
  • Uba Sani ya bayyana cewa yana da ƙudirin ganin cewa ya bar jihar Kaduna fiye da yadda ya same ta a lokacin da ya hau madafun iko
  • Gwamnan ya nuna gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka masu tarin yawa domin bunƙasa walwala da jin daɗin mutanen Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana ƙudirin da yake da shi kan jihar kafin ya bar mulki.

Gwamna Uba Sani ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa tana da ƙudurin barin jihar Kaduna a mafi kyawun yanayi fiye da yadda ya same ta.

Uba Sani ya sha alwashi a Kaduna
Uba Sani ya ce yana son barin Kaduna fiye da yadda ya same ta Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Gwamnan ya yi wannan alƙawari ne yayin ƙaddamar da aikin ginawa da faɗaɗa titunan cikin garin Zaria, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Wani bawan Allah ya faɗi ana tsakiyar sallah a masallaci, ya rasu a watan azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani na ayyuka a jihar Kaduna

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ƙara azama wajen aiwatar da shirin canza yankunan karkara, inda ta ƙaddamar da fiye da ayyukan gina tituna 78 a faɗin jihar Kaduna tun bayan hawansa mulki.

Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa ayyukan suna tafiya yadda ya dace, domin an samar da isassun kuɗaɗe ga ƴan kwangila don kammala su cikin wa’adin da aka tsara.

Ya ce manufarsa ita ce haɗa al’ummomi don samar da fa’idoji na zamantakewa da tattalin arziƙi.

“Da zarar an kammala, waɗannan titunan cikin garin Zaria za su amfanar da al’ummar birnin, musamman talakawan da ke zaune a wuraren."
"Za a samar da damar ayyukan yi, harkokin kasuwanci za su inganta sosai, sannan tsaro zai ƙara ƙarfafa a birnin da kewaye.”

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa Zaria tana da matuƙar muhimmancin da ba za a bar ta a halin da take ciki ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi sharadin karban tuban 'yan ta'adda irinsu Bello Turji

Ya nuna cewa ƙaddamar da wannan aiki wata alama ce ta jajircewarsu wajen gina sababbin hanyoyi da kuma faɗaɗa su, gyara da kula da hanyoyin da ake da su, domin sauƙaƙa sufuri da bunƙasa kasuwanci a faɗin jihar.

An yi wa Uba Sani alƙawarin ƙuri'u

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Zaria, Jamil Ahmad, ya ce mutanen Zaria za su ƙara yawan ƙuri’unsu ga Gwamna Uba Sani a 2027 idan ya bayyana niyyar sake tsayawa takara.

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa Gwamna Uɓa Sani bisa aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a faɗin jihar.

Kwamishinan Uba Sani ga gargaɗi El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarauta na jihar Kaduna, ya yi wa Malam Nasir El-Rufai kashedi.

Sadiq Mamman Lagos ya bayyana cewa tsohon gwamnan bai da hurumin yanke abin da zai faru a zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa kalaman da El-Rufai ya yi game da gwamna Uba Sani da shugaba Bola Tinubu ko kaɗan ba su dace ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng