Sheikh Jabir Maihula: Abubuwa 5 da Ake Tunanin Suna Karya Azumi alhali ba Su Karyawa

Sheikh Jabir Maihula: Abubuwa 5 da Ake Tunanin Suna Karya Azumi alhali ba Su Karyawa

Sokoto - Fitaccen malamin addinin musulmi a jihar Sakkwato, Sheikh Jabir Sani Maihula ya yi bayani kan wasu abubuwa guda 5 da ba su karya azumin Ramadan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A cikin ibadu da addinin Musulunci ya wajabta, azumin watan Ramadan yana da muhimmanci sosai.

Dr. Jabir Sani Maihula.
Sheikh Jabir Maihula ya yi bayani kan wasu abubuwa da ake tunanun suna karya azumi Hoto: Dr. Jabir Sani Maihula
Asali: Facebook

A wannan wata na azumi, musulmai na kamewa daga cin abinci da sha daga ketowar alfijir har zuwa faɗuwar rana, kamar yadda BBC Hausa ta kawo.

Duk da haka, akwai wasu abubuwa da mutane ke tunanin suna karya azumi, alhali kuwa ba haka ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Jabir Maihula, ya bayyana wasu abubuwa biyar da ake yawan ɗauka cewa suna karya azumi, amma bisa sharuddan shari’a ba sa karya shi.

1. Fitar maziyyi bai karya azumi

Daga cikin abubuwan da ake ce-ce-kuce a kansu akwai fitar maziyyi. Malamin ya bayyana cewa maziyyi wani ruwan sha'awa ne da ke fita daga namiji ko mace ba tare da sun yi jima'i ba.

Kara karanta wannan

An yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya kan hutun azumi a makarantun Arewa

Ya kan bayyana ne sakamakon tunani ko kallon wani abu da ke tayar da sha’awa. Bisa fatawowi mafi inganci, fitar maziyyi ba ya karya azumi.

"Wani lokacin ya kan fita ba tare da ka sani ba saboda yana fita kaɗan-kaɗan, bisa fatawa mafi inganci fitar maziyyi ba ya karya azumi," in ji Sheikh Jabir.

2. Amfani da man goge baki da tsakar rana

Wasu masu azumi kan guji amfani da man goge baki da burushi saboda tsoron karya azuminsu, wasu kuma suna so su riƙe warin baki domin samun ladan da hadisi ya ambata.

Sai dai, Sheikh Maihula ya bayyana cewa, bisa fatawar manyan malamai irin su Sheikh Ibn Uthaimin da Ibn Baz, amfani da man goge baki ba ya karya azumi, matuƙar ba a haɗiye shi ba.

Malamin ya ci gaba da cewa,

"Man goge baki ba abin ci ko na sha ba ne, kuma ba ya kaiwa ciki - sai dai fa idan mutum haɗiyewa ya yi da gangan."

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan Jigawa ya kai ziyara wajen raba abinci, ya gano abin mamaki

3. Ɗibar jini ko yin allura da azumi

A cewar malamin, idan mutum yana buƙatar a ɗauki jininsa don yin gwaji, hakan ba ya karya azumi.

Sai dai babban malamin ya ja hankalin musulmi da kada su bayar da jini domin ƙara wa wani alhali suna azumi, domin akwai saɓani a kan hakan.

Game da yin allura, ya ce ba ta karya azumi muddin ba allurar da ake amfani da ita a matsayin abinci ba ce.

4. Shaƙa maganin asma da rana

Mutanen da ke fama da cutar asma sukan yi amfani da inhaler watau maganin shaƙawa don sauƙaƙa yanayin numfashinsu.

Sheikh Jabir Maihula ya bayyana cewa yin amfani da wannan magani ba ya karya azumi, domin ba abinci ba ne, ba kuma abin sha ba ne.

5. Amfani da maganin ciwon ido

Sheikh Maihula ya ƙara da cewa amfani da maganin da ake ɗigawa a ido ba ya karya azumi, koda kuwa mutum ya ji ɗanɗanonsa a maƙogwaro.

Kara karanta wannan

'Muna cikin tashin hankali': Daruruwan mata sun fita zanga zanga a jihar Benuwai

Malamin ya ce maganin ciwon idon ba wani abu ba ne da ke zuwa ciki kamar abinci ko abin sha.

A taƙaice, wadannan abubuwa na daga cikin shubuhohi da ake yawan samun saɓani a kansu, amma bisa fatawar masana, ba sa karya azumi.

Hanzari ba gudu ba

Sai dai, duk da haka akwai wasu nau'ikan abubuwan da ka iya karfa azumi, musamman magunguna masu aiki a matsayin abinci.

Malamai da dama sun yi fatawowi kan nau'ikan magungunan da za a iya amfani da su a azumi da kuma wadanda ka iya zama barazana ga azumin.

Idan baku manta ba, azumi ibada ne da Musulmai ke yi don neman kusanci da Allah, wanda ke nufin kauracewa cin abinci, shan ruwa, jima'i da dukkan abubuwan da ke kama da wadannan.

Sheikh Guruntum ya buɗe masallaci

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum ya bude sabon masallacinsa da aka fi sani da Masjidud Da’awah a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Faɗa ya kaure da mutanen gari kan ruwan sha a watan azumi, an yi kisa

An shirya taron kaddamar da masallacin domin gudanar da addu’o’i tare da karatuttukan manyan malamai daga sassa daban-daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar kara bayani kan abubuwan da ka iya karya azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262