Rai Bakon Duniya: Kwamishina Mai Ci a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnatin Abia ta sanar da rasuwar Sunny Onwuma, 'dan majalisar zartarwa kuma kwamishinan kwadago da samar da ayyukan jihar
- Sanarwar ta ce Onwuma, wanda ya fito daga Ihie a karamar hukumar Ugwunagbo, ya rasu bayan gajerar rashin lafiya yana da shekaru 61
- Gwamnati ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin da daukacin jama’ar Abia, tana addu’a Allah ya ji kan shi, ya bai wa iyalansa hakuri
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Gwamnatin jihar Abia ta sanar da rasuwar Sunny Onwuma, mamba a majalisar zartarwa ta jiha kuma kwamishinan kwadago da samar da ayyuka.
Prince Okey Kanu, kwamishinan yada labarai na jihar, ya bayyana cewa kwamishinan ya rasu a safiyar Litinin, 3 ga watan Maris, 2025.

Source: Twitter
Kwamishinan Abia, Sunny Onwuma ya rasu
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook, Prince Okey ya nuna cewa kwamishinan kwadago da samar da ayyuka na jihar Abia, ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa, marigayin, wanda dan asalin garin Ihie ne da ke a karamar hukumar Ugwunagbo, ya yi karatu a kwalejin gwamnatin Umuahia da jami'ar Abia da ke Uturu.
Sanarwar kwamishinan yada labaran ta kara da cewa Onwuma ya kasance dan jam’iyyar LP, kuma shugaba nagari da ke da girman daraja a al’ummarsa.
Prince Okey Kanu ya ruwaito cewa Onwuma ya rasu yana da shekaru 61 a duniya kuma ya mutu ya bar mata da ‘ya’ya hudu.
Gwamnatin jihar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa, da daukacin jama’ar Jihar Abia.
Iyalai za su fadi lokacin jana'izar kwamishinan

Source: Facebook
Cikakkiyar sanarwar da kwamishinan yada labaran ya fitar ta ce:
"Cike da alhini amma cikin cikakken yarda da kudirar Ubangiji, gwamnatin jihar Abia take sanar da rasuwar Kwamared Sunny Nwanganga Onwuma, mamba na kwamitin zartarwa na jihar kuma kwamishinan kwadago da samar da ayyuka.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
"Kwamared Onwuma ya rasu da safiyar Litinin, 3 ga Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya.
"Marigayin dan asalin Ihie ne a karamar hukumar Ugwunagbo ta jihar Abia. Ya halarci kwalejin gwamnati ta Umuahia da jami’ar jihar Abia, Uturu. Shi dan jam’iyyar LP ne na kwarai kuma shugaba mai daraja a cikin al’ummarsa.
"Ya rasu yana da shekaru 61 a duniya, kuma ya bar mata da ‘ya’ya hudu.
"Gwamnatin jihar Abia tana mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da daukacin jama’ar jihar. Muna addu’a Allah ya jikan shi, ya kuma bai wa iyalansa karfin hali don jure wannan babban rashi.
"Iyalan marigayin za su sanar da shirye-shiryen jana’iza a nan gaba."
Kwamishiniyar mata ta riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bayelsa ta sanar da rasuwar kwamishiniyar harkokin mata, Elizabeth Bidei, wacce ta kasance 'yar majalisar zartarwa ta jihar.
Gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa, ta mika ta'aziyya ga iyalanta, musamman mijinta, Cif Jackson Bidei, da ‘ya’yansu, tare da addu’ar Allah ya jikan ta.
Gwamnatin ta yaba da jajircewar marigayiyar wajen inganta rayuwar mata a jihar, tana mai cewa za a ci gaba da tunawa da gudunmuwarta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

