'Yan Sanda Sun Cafke Jami'an NDLEA a Kano, An Gano Laifinsu
- Ƴan sanda a jihar Kano sun cafke wasu jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) guda biyu
- An cafke jami'an na hukumar NDLEA ne bisa zargin harbe wata yarinya har lahira a unguwar Jaba Quarters da ke Kano
- Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin wanda ya kai ga rasuwar yarinyar mai shekara 19, ya auku ne a daren ranar Laraba
- Kakakin hukumar NDLEA na jihar Kano, ya ce sun fara gudanar da bincike domin a iya gano haƙiƙanin abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda ta cafke wasu jami’ai biyu na hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Kano.
Ƴan sandan sun cafke jami'an na NDLEA ne bisa zargin harbe wata yarinya mai shekara 19, mai suna Patient Samuel har lahira a unguwar Jaba Quarters.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan sanda suka cafke jami'an NDLEA
Majiyoyi sun bayyana cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ce ta kama jami’an na NDLEA, suka ce lamarin harbin ya faru ne a daren ranar Laraba misalin ƙarfe 10:55 na dare.
Majiyoyin sun ce wata tawagar jami’ai sun je wurin da lamarin ya faru, suka ɗauki Patient Samuel zuwa asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, aka tabbatar da rasuwarta.
Ƴan sandan dai sun kama jami’ai biyu na NDLEA, Nass Ridwan Usman, mai shekara 23, da Sna Ismaila Yakubu, mai shekara 26, waɗanda ke aiki a hedkwatar hukumar a Kano.
Kayayyakin da aka samu a hannunsu sun haɗa da babur ɗinsu na aiki, harsashi ɗaya, harsasai guda huɗu masu kaurin 7.62×51mm waɗanda babu komai a cikinsu da kuma wuƙaƙe guda biyu.
Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan sanda sun fara bincike don gano haƙiƙanin dalilan da suka haddasa harbin.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya tabbatar da cafke jami'an na NDLEA, kuma ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar bincike.
Hakazalika, kakakin NDLEA reshen jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
"Muna bincike a kan lamarin, da za ran mun kammmala gano gaskiyar abin da ya faru, za mu fitar da sanarwa."
- Sadiq Muhammad Maigatari
Jami'an NDLEA sun cafke ɗan shekara 75 a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun cafke wani dattijo mai shekara 75 a jihar Kano.
Jami'an na NDLEA sun cafke dattijon ne mai suna Nuhu Baba, kan zargin siyar da miyagun ƙwayoyi da kayan maye.
An dai cafke dattijon ne yayin wani samame da jami'an hukumar suka kai a ƙauyen Tumbau da ke ƙaramar hukumar Gezawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng