'Dalilin da Ya Sa Koken Natasha na Cin Zarafi ba Zai Samu Karɓuwa ba a Majalisa'

'Dalilin da Ya Sa Koken Natasha na Cin Zarafi ba Zai Samu Karɓuwa ba a Majalisa'

  • Takaddama ta barke a majalisa bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da koken cin zarafin da ta ce Godswill Akpabio, ya yi mata
  • Wasu Sanatoci sun ki amincewa da kokenta, suna cewa ba a bi ka’idojin majalisa ba, yayin da wasu ke goyon bayanta kan zargin da take yi
  • Sanata Tahir Monguno ya ce dokar majalisa ba ta yarda a tattauna batun da ke kotu ba, tun da Natasha da matar Akpabio duk sun kai kara
  • Natasha ta musanta cewa ta kai kara kan cin zarafi, ta bukaci Akpabio ya amince da koken nata domin a mika shi ga kwamitin ladabtarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da korafin cin zarafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Sai dai takaddama ta barke kan hanyoyin da ita Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bi wajen shigar da koken.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Sanata ya tono sirri a baya da Natasha ke zargin tsohon gwamna da cin zarafi

An yi fatali da korafin Natasha a majalisa
Sanatoci sun yi fatali da koken Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin Godswill Akpabio. Hoto: The Nigeria Senate.
Asali: Twitter

Wasu Sanatoci sun yi watsi da korafin Natasha

Punch ta ce Akpoti-Uduaghan ta shigar da korafi bayan mai magana da yawun majalisa, Yemi Adaramodu, ya ce koken da ke gabanta shi ne na saba doka da Sanatar ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki ya haifar da cece-kuce, inda magoya bayan Akpoti-Uduaghan suka fito kwansu da kwarkwatarsu suna neman adalci da murabus din Akpabio.

Wasu sanatoci sun goyi bayan Akpabio, suna cewa koken bai bi ka’idojin majalisa ba, duk da Shugaban Majalisar ya yanke hukunci kan batun sauraron koken.

Sanata Monguno ya ce bisa ga Dokar Majalisa, ba a tattauna batun da ke gaban kotu, cewar BusinessDay.

Monguno ya ce:

“Natasha ta kai kara, haka matar Akpabio ma ta kai, don haka ba mu da hurumi.”
Natasha ta shigar da korafi majalisa kan zargin cin zarafi
Majalisa ta ki amincewa da korafin Natasha Akpoti-Uduaghan kan rashin bin ka'idoji. Hoto: @NGRSenate.
Asali: Twitter

Abin da dokar majalisa ta ce kan lamarin

Sanata Yahaya Abdullahi ya bukaci a mika batun ga kwamitin ladabtarwa domin duba sahihancin dokar da Sanata Monguno ya ambata.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Sanata Opeyemi Bamidele ya ce dokar majalisa ta hana Sanata ya shigar da kokensa da kansa.

Bamidele ya ce:

“Dole a shigar da korafi ne a madadin jama’a, ina tausayawa Shugaban Majalisa a matsayin wanda ake zargi, amma hukumomi za su yi aikinsu.”

Akpoti-Uduaghan ta musanta cewa koken nata yana kotu, ta ce wanda ke gaban kotu shi ne karar cin mutuncin da hadimin Akpabio ya shigar.

Ta bukaci Akpabio ya karɓi koken domin a mika shi ga kwamitin da ke binciken irin waɗannan batutuwa.

Akpabio ya musanta zargin cin zarafi, yana mai cewa:

“Ba zan taba cin zarafin wata mace ba saboda mahaifiyata ta ba ni tarbiyya sosai.”

Ya ce tun ranar 25 ga Fabrairu ya fara samun kira kan batun, amma ya bukaci ‘yan Najeriya su jira hukuncin kotu.

Kotu ta hana majalisa binciken Natasha

Kun ji cewa Kotu ta dakatar da Kwamitin Majalisar Dattawa daga bincikar Natasha Akpoti-Uduaghan kan batun ladabtar da ita.

Kara karanta wannan

Zargin Akpabio: Kotu ta kawo cikas ga majalisa kan binciken Sanata Natasha

Wannan hukunci ya hana kwamitin ci gaba da shirin dakatar da Sanatar har sai an sake duba shari'ar da ke gabanta kafin aiwatar da hukuncin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng