Duk da Korafin CAN a Jihohi, An Fara Hutun Azumin Ramadan a Jami'ar Tarayya
- Rahotanni na nuni da cewa jami’ar Maiduguri ta sauya jadawalin lokacin aiki domin dacewa da azumin Ramadan
- Za a fara aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, sai daga 8:00 zuwa 2:00 a ranar Jumu’a
- Baya ga haka, hukumomi a jami’ar sun bukaci ma’aikata da dukkan dalibai su bi sabon tsarin yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta sanar da sauya jadawalin lokacin aiki domin bai wa ma’aikata da daliban da ke azumin Ramadan damar gudanar da ibadarsu cikin sauki.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da Malam Malah daga sashen kula da harkokin jama’a ya fitar a ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025.

Asali: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa dokar rage lokacin za ta fara aiki nan take daga lokacin da jami'ar ta fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauyin lokacin aiki zai bai wa ma’aikata da dalibai damar hada ibada da aikin karatu cikin natsuwa, la’akari da cewa azumin Ramadan na bukatar juriya.
Sabon jadawalin aiki a jami'ar Maiduguri
A cewar sanarwar, sabon tsarin zai fara aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, yayin da a ranar Jumu’a za a rufe aiki da karfe 2:00 na rana.
Jami’ar ta bayyana cewa wannan sauyi zai taimaka wa ma’aikata da dalibai wajen samun damar yin ibada da gudanar da ayyukansu ba tare da wahala ba.
A cewar jami'ar:
“An yi wannan sauyi ne domin ba wa masu azumi damar gudanar da ibadarsu cikin sauki, tare da rage nauyin aiki a wannan wata mai alfarma,”
Jami’ar ta kuma bukaci ma’aikata da dalibai da su kiyaye sabon jadawalin, domin tabbatar da aiki ba tare da tangarda ba.
Bukatar yin ibada a watan Ramadan
Ramadan wata ne da Musulmai ke amfani da shi wajen kusantar Allah ta hanyar azumi, ibada da sauran ayyukan alheri.
Sanarwar jami’ar ta bayyana cewa wannan lokaci yana da matukar muhimmanci ga dalibai da ma’aikata domin yin ibada tare da ci gaba da gudanar da aikinsu.
Sanarwar da jami'ar ta fitar ya yi nuni da cewa:
“Azumin Ramadan lokaci ne na sadaukarwa da juriya, don haka dole a daidaita yanayin aiki da bukatun addini,”
Jami’ar ta ce tana da kwarin gwiwa cewa wannan sabon jadawalin zai taimaka wajen inganta jin dadin masu azumi, tare da tabbatar da cewa ayyukan jami’ar na tafiya yadda ya kamata.

Asali: Original
Hukumar jami’ar ta bukaci ma’aikata da dalibai da su hada kai wajen ganin an bi sabon tsarin yadda ya kamata.
Azumi: An rage lokutan aiki a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa, gwamnatin jihar Jigawa ta rage lokutan aiki ga ma'aikatan gwamnati.
A ranar Talata gwamnatin Malam Umar Namadi ta fitar da sanarwar, inda ta ce hakan na cikin kokarinta na samar da walwala ga jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng