'Dan Bindiga Ya Tono Sirrin 'Yan Ta'adda ga Sojoji kafin 'Yan Uwansa Su Harbe Shi

'Dan Bindiga Ya Tono Sirrin 'Yan Ta'adda ga Sojoji kafin 'Yan Uwansa Su Harbe Shi

  • Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin kwanton-bauna da ‘yan bindiga suka yi a dajin Kwassau, yankin Kagarko a jihar Kaduna
  • An kashe Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, daya daga cikin manyan masu garkuwa da mutane a yankin
  • Hakan na zuwa ne bayan an kama Dogo Saleh a ranar 9 ga watan Janairu 2025, wanda ya saba garkuwa da mutane da kashe jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Jami’an tsaro sun samu nasarar dakile wani yunkurin ‘yan bindiga na kwanton-bauna a dajin Kwassau da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

A yayin gwabzawa da suka yi, sun kashe wani fitaccen mai garkuwa da mutane, Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta tsallaka, ta kai harin ramuwar gayya a Neja, ta kashe bayin Allah

Sojoji
An kashe hatsabibin dan bindiga a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa tun bayan kama shi, jami’an tsaro sun gudanar da bincike mai zurfin da ya kai ga nasarar dakile hare-haren ‘yan bindiga da kuma kama wasu daga cikin su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama Dogo Saleh da ke aiki a matsayin babban jami’i ga wani babban dan ta’adda mai suna Boka a kan hanyar Abuja-Kaduna.

Sirrin da Dogo Saleh ya tono ga sojoji

Bayan kama shi, Dogo Saleh ya amsa cewa ya jagoranci garkuwa da mutane da dama a kan hanyar Lokoja-Abuja, tare da wata tawaga da ta kunshi mayaka 100 dauke da manyan makamai.

Ya bayyana cewa kungiyar su na da manyan makamai da suka hada da bindigogi nau’in AK-47, GPMG da kuma bindigogin harbo jirgin sama.

Ya ce daga cikin garkuwar da suka yi, akwai wata ‘yar sanda da ‘ya’yanta da kuma wani jami’in kwastam da matarsa.

Har ila yau, ya amsa cewa shi ne ya jagoranci harin da aka kai a shingen jami’an sojan ruwa a ranar 5 ga watan Janairu 2025, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu da kwace makamai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga

Bisa la’akari da bayanan da Dogo Saleh ya bayar, jami’an tsaro sun kaddamar da wani farmaki domin cafke wani babban dan ta’adda mai suna Abdu Musa, wanda aka fi sani da Kanabaro.

Da misalin karfe 11:01 na dare, yayin da tawagar jami’an tsaro ke kokarin kai farmaki a dajin Kwassau, sai wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton-bauna da nufin kubutar da Dogo Saleh.

Bayan musayar wuta, ‘yan bindigar sun tsere da raunuka, yayin da Dogo Saleh ya samu munanan raunuka sakamakon harbin da abokan aikinsa suka yi masa cikin rudani.

Hafsun tsaro
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Musa. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Dogo Sale ya mutu sakamakon harbi

An garzaya da Dogo Saleh zuwa Asibitin Gwamnati da ke Kubwa, daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

Wani jami’in tsaro, mai suna Suleiman Adamu daga rundunar yaki da masu garkuwa da mutane, ya samu raunuka kadan a yayin fafatawar, amma an yi masa magani kuma an sallame shi.

Kara karanta wannan

Ana neman Turji, wani ɗan bindiga da yaransa sun ba da mamaki, sun mika wuya

A yayin farmakin, jami’an tsaro sun kwato bindigar AK-47 da kuma tarin harsasai daga hannun 'yan ta'addan.

Bayan artabun, jami’an tsaro sun kara karfafa sintiri da kuma sa ido a yankin Kagarko da manyan hanyoyi domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere.

Barayi sun sace babura a masallaci a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu barayi sun tafka sata a masallaci yayin da Musulmai ke tsaka da sallar tarawihi a Abuja.

Rahoton Legit ya nuna cewa barayin sun sace babura uku kuma an mika rahoto wajen kungiyar 'yan acaba domin ganin an kama su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng