Zargin Akpabio: Kotu Ta Kawo Cikas ga Majalisa kan Binciken Sanata Natasha

Zargin Akpabio: Kotu Ta Kawo Cikas ga Majalisa kan Binciken Sanata Natasha

  • Kotu ta dakatar da Kwamitin Majalisar Dattawa daga bincikar Natasha Akpoti-Uduaghan kan batun dakatar da ita
  • Wannan hukunci ya hana kwamitin ci gaba da shirin dakatar da Sanatar har sai an sake duba shari'ar da ke gabanta
  • Sanata Natasha ta nemi binciken da za a yi mata ya kasance a bude domin kowa ya gani ba tare da an yi nuku-nuku ba
  • Har yanzu ana jiran karin bayani kan matakin da za a dauka a majalisar dattawan bayan hukuncin da kotu ta bayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotu ta shiga lamarin dambarwar da ke wakana tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisa, Godswill Akpabio.

Kotun ta bayar da umarni na wucin gadi da a dakatar da Kwamitin Ladabtarwa na Majalisar Dattawa daga bincikar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Kara karanta wannan

Natasha: An hura wutar sauke Akpabio, Barau zai iya zama shugaban majalisa

Kotu ta dauki mataki kan majalisa game da binciken Natasha
Kotu ta dakatar da majalisa kan shirin binciken Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Hoto: Natasha H Akpoti, Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

Zargin da Sanata Natasha ke yi wa Akpabio

Tribune ta ce wannan hukunci ya zo ne yayin da kwamitin ke shirin zaman da zai yanke shawara kan dakatar da Sanatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan Natasha ta yi zargin cewa Akpabio ya sha neman yin lalata da ita domin samun fifiko game da kudurorinta.

Natasha ta tabbatar da cewa ta ki amincewa da bukatarsa wanda yake amfani da hakan wurin fatali da duk wata bukata ta ci gaban yankinta a majalisar.

Martanin Akpabio kan zargin da ake yi masa

Daga bisani, Akpabio ya musanta wannan zargi inda yake cewa ta yi hakan ne kawai domin ta bata masa suna.

Mai magana da yawun shugaban majalisar, Kenny Okulogbo shi ya musanta zargin, yana mai cewa karya ce kuma ba ta da tushe.

Natasha ta samu sauki bayan hukuncin kotu kan zargin Akpabio
Kotu ta dakatar da majalisa kan binciken Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Hoto: Natasha H Akpoti.
Asali: Twitter

Natasha/Akpabio: Wane mataki kotu ta ɗauka?

A cewar hukuncin kotu, ba za a iya ci gaba da binciken ba har sai an sake duba shari'ar gaba daya, cewar jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Alamar rauni ne: Tsohuwar Sanata ta dura kan Natasha game da zargin Akpabio

Wannan mataki ya kawo cikas ga shirin da Majalisar Dattawa ke yi na daukar mataki a kan Sanatar Natasha.

Sanata Natasha ta bukaci cewa binciken da za a yi mata ya kasance a bude don jama’a su shaida abin da ke faruwa.

Wannan bukata ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan siyasa da jama’a wanda ya hargitsa kafofin sadarwa duba da martabar majalisar.

Har yanzu ba a bayyana matakin da Majalisar Dattawa za ta dauka ba bayan wannan hukunci na kotu.

Ana jiran karin bayani daga bangaren shari’a da kuma Majalisar Dattawa dangane da ci gaban lamarin.

Yadda wata ta zargi Akpabio a baya

Mun ba ku labarin cewa a baya, tsohuwar shugabar NDDC, Joy Nunieh, ta zargi Godswill Akpabio da cin zarafi, ta ce ta mare shi a gidansa a Apo da ke birnin Abuja.

Sanata Akpabio ya musanta zarge-zargen da ake yi masa inda ya fayyace rigimar da cewa an cire Nunieh daga mukaminta ne saboda dalilin rashin da’a.

Kara karanta wannan

Yaɗa bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure wasu 'yan TikTok 2 a Kano

Wannan na zuwa ne bayan arangama da ta faru tsakanin Natasha da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a yan kwanakin nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng