Shugaban NAHCON Ya Sha Sabon Alwashi kan Aikin Hajjin 2025
- Shugaban hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Saleh, ya kwantar da hankalin ƴan Najeriya kan aikin Hajjin 2025
- Farfesa Abdullahi Saleh da aka fi sani da Pakistan ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta ba shugaba Bola Tinubu da ƴan Najeriya kunya ba
- Shugaban na NAHCON ya ba da tabbacin cewa shirye-shirye sun yi nisa domin ganin cewa an gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya sha alwashi kan aikin Hajjin 2025.
Shugaban na NAHCON ya yi alƙawarin cewa ba zai ba shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƴan Najeriya kunya ba wajen cimma burinsa na gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON za ta ba da kunya ba
Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana cewa hukumar na da niyyar sauke nauyin da ke kanta, musamman na aikin Hajjin 2025.
Ya ce an shirya dukkan abubuwan da suka dace don tabbatar da cewa Hajjin 2025 zai kasance cikin nasara, yana mai cewa dukkan maniyyatan da aka yi wa rajista za su mori kuɗinsu.
Shugaban ya ƙara da cewa hukumar NAHCON tana ci gaba da samun nasarori masu muhimmanci wajen kyautata ayyukan Hajji ga dukkan maniyyatan Najeriya.
Shugaban NAHCON ya ba Tinubu tabbaci
"Ina so na tabbatarwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa NAHCON ƙarƙashin kulawata ba za ta bari shi da ƴan Najeriya su ji kunya ba, domin aikin Hajjin 2025 zai gudana cikin nasara."
"Haka kuma, ina tabbatarwa da ƴan Najeriya, musamman maniyyatan da ke shirin tafiya, cewa za su godewa shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumar NAHCON saboda aikin Hajjin 2025."

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka
"Shugaban ƙasan ya cika alƙawarinsa. Yana ba mu dukkan goyon bayan da muke buƙata. Ba za mu yi wasa da amanar da ya bamu ba. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba a kan aikinmu."
"Saboda haka, dole ne mu godewa shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima saboda amanar da suka ba mu don jagorantar harkokin aikin Hajji."
"Hukumar ta samu wasu nasarori, wanda mafi muhimmanci shi ne dawo da fiye da N5bn na abubuwan da aka kasa yi wa Alhazai a lokacin aikin Hajjin 2023."
"Haka kuma, muna aiki tare da hukumar shige da fice ta Najeriya don tabbatar da bayar da fasfo ga maniyyatan da ke shirin tafiya a kan lokaci."
Hakazalika Farfesa Abdullahi Saleh ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su ci gaba da tallafawa manufofin hukumar.
NAHCON ta fara ɗaukar ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da fara ɗaukar ma'aikata domin aikin Hajjin shekarar 2025
Hukumar NAHCON za ta ɗauki likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na wucin gadi domin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Za a ɗauki ma'aikatan ne domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu kulawar da ta dace a lokacin da suke sauke farali a ƙasa mai tsarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng