An Kafa Tarihi: TCN Ya Taka Sabon Matsayi na Samar da Wutar Lantarki a 2025

An Kafa Tarihi: TCN Ya Taka Sabon Matsayi na Samar da Wutar Lantarki a 2025

  • Kamfanin TCN ya sanar da cewa an kai megawatt 5,713.6 na samar da hasken lantarki ranar 2 ga Maris, 2025, wanda ya zarce matsayin baya
  • Amma kamfanin ya ce duk da haka, wannan ci gaba bai kai matsayin mafi girma da aka taba cimmawa ba na megawatt 5,801.60 a shekarar 2021
  • Sanarwar da kamfanin ya fitar ta yi nuni da cewa duk da haka, an samu gagarumar nasara a tarihin samar da hasken wuta a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa Najeriya ta cimma sabon matsayi a samar da wutar lantarki a 2025, bayan samar da wuta megawatt 5,713.6.

A cikin wata sanarwa da TCN ya fitar a ranar Talata, kamfanin ya bayyana cewa an cimma wannan matsayin ne a ranar 2 ga Maris da karfe 9:30 na dare.

Kara karanta wannan

Ana ciyar da mabukata a Kano, mutane 91,000 za su samu buda-bakin Ramadan

Hasken wuta
An samu rarraba hasken wuta mafi yawa a Najeriya a cikin kwanakin nan Hoto: Transmission Company of Nigeria
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan sabon adadi ya zarce wanda aka samar a baya da megawatt 170.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya dai, kamfanin TCN ya bayyana cewa an yi nasarar samar da hasken wutar lantarki megawatt 5,543 a ranar 14 ga Fabrairu, 2025.

Wutar lantarki: TCN ya taka sabon matsayi

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa TCN ya bayyana gamsuwarta da wannan ci gaba da aka samu a bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya.

Kamfanin ya bayyana cewa:

"An samu wannan ci gaba ne a ranar Lahadi, 2 ga Maris, 2025, da karfe 9:30 na dare, inda sabon matsayi na megawatt 5,713.60 ya zarce matsayi na baya da megawatt 170.40. Matsayi na baya dai shi ne megawatt 5, 543.20 wanda aka cimma a ranar 14 ga Fabrairu, 2025."
Lantarki
An raba megawatt sama da 5, 500 a rana guda Hoto: Transmission Comapny of Nigeria
Source: Facebook

TCN ya kara da cewa duk da wannan sabon ci gaba, bai kai matsayi mafi girma da aka taba cimmawa a tarihi ba, wanda ya kai megawatt 5,801.60 a ranar 1 ga Maris, 2021, da megawatt 88.

Kara karanta wannan

Masu safarar yara sun yiwa 'yan sandan Najeriya tayin cin hancin Naira miliyan 1

Duk da haka, kamfanin ya bayyana cewa wannan sabon matsayi babbar nasara ce da aka cimma a sashen samar da hasken wuta a kwanakin nan.

"An samu karuwar hasken wuta" - TCN

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki (TCN) ya bayyana cewa an samu matsayi mafi girma a adadin wutar da aka samar a rana daya a tarihin masana’antar wutar lantarki ta Najeriya.

A cewar kamfanin:

"An kafa sabon matsayi mafi girma a adadin wutar da aka samar a rana daya a tarihin masana’antar wutar lantarki ta Najeriya a jiya, inda aka samar da jimillar megawatt 125,542.06."

Kamfanin ya kara da cewa wannan sabon adadi ya zarce wanda aka cimma a baya, wanda shi ne 125,159.48MWh a ranar 14 ga Fabrairu, 2025, da megawatt-hours 382.58.

TCN ya ce wannan ci gaba yana nuna kokarin da ake yi domin inganta samar da wutar lantarki a Najeriya, wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da rayuwar al’umma.

TCN: "Babu wuta a fadar shugaban kasa"

A baya, kun samu labarin cewa an samu matsalar wutar lantarki a birnin Abuja sakamakon tangardar wasu layukan wuta na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC).

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, NNPCL ya yi maganar saukar farashin fetur da kara gidajen mai

Wannan matsala ta haddasa katsewar wuta a akalla wurare 53 a babban birnin tarayya, ciki har da Fadar Shugaban kasa, amma kamfanin TCN ya ce injiniyoyinsa na kokarin gyara matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng