'Farashin Man Fetur zai Cigaba da Sauka a fadin Najeriya'
- Masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya ce farashin man fetur zai ci gaba da saukowa har zuwa watan Yunin 2025
- Ya yi magana ne bayan Dangote da NNPCL sun rage farashin fetur, wanda hakan zai rage radadin wahala ga ’yan Najeriya
- Bismarck Rewane ya ce gogayya da ake yi a kasuwa tsakanin Dangote da NNPCL za ta amfanar da masu sayen fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Farashin man fetur a Najeriya na ci gaba da saukowa sakamakon rage farashin da manyan masu samar da shi suka yi, ciki har da matatar Dangote da NNPCL.
Masani a fannin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya bayyana cewa ana sa ran ci gaba da samun raguwar farashin har zuwa watan Yunin shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Asali: Getty Images
A wata hira da ya yi da Channels Television a ranar Talata, Rewane ya ce saukar farashin zai ci gaba har sai kasuwar mai da canjin kudi sun sauya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rewane: 'Farashin fetur zai cigaba da sauka'
Bismarck Rewane ya ce matakin rage farashin fetur da matatar Dangote da NNPCL suka dauka zai ci gaba da amfanar da masu amfani da shi.
"Za mu ci gaba da ganin saukar farashi daga yanzu har zuwa Yuni. Bayan haka, farashin na iya sauyawa gwargwadon yadda kasuwar mai da canjin kudi suka kasance,"
- Bismarck Rewane
Gasa tsakanin Dangote da NNPCL
Masanin ya kara da cewa yadda Dangote da NNPCL ke gasa a kasuwa zai kara rage farashin a kasuwar fetur.
Rewane ya bayyana cewa gasar sauke farashin man fetur da ake tsakanin matatar Dangote da NNPCL ta na amfanar 'yan Najeriya.
Bismarck Rewane ya ce:
"A gasar sauke farashi da ake, babu wanda ke cin riba sai masu amfani da mai."
Bismarck Rewane ya ce sauke farashin da matatar Dangote ke yi na da nasaba da yadda kamfanin ke inganta tsarin samar da fetur a cikin gida.
Yadda farashin fetur ke sauka a Najeriya
A kwanakin baya, Kamfanin Dangote ya rage farashin fetur daga ₦890 zuwa ₦825 a kowace lita a matatarsa.
Matatar Dangote ta kuma bada tabbacin mayar da kudi ga kwastomomin da suka saye fetur a kan tsohon farashi daga wuraren da ke karkashinta.
Haka zalika, a ranar Litinin, NNPCL ta rage farashin fetur zuwa ₦860 a a gidajen manta na birnin Legas, duk da cewa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan hakan.
Legit ta tattauna da dan acaba
Wani dan acaba a jihar Gombe, Muhammad Ibrahim ya ce za su yi farin ciki da saukar farashin matukar aka cigaba da samunsa.
"Duk da cewa saukin da ake samu a yanzu ba sosai ba ne, idan aka cigaba da samun ragi za mu yi farin ciki sosai.
Wani lokaci kana son yi wa mutane sauki, amma idan ka tuna kudin fetur sai hakan ya gagara. Idan farashin fetur ya sauka mu ma za mu fi jin dadin aikin."
- Muhammad Ibrahim

Asali: Getty Images
Wuraren da ake sumun man Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta bayyana wuraren da ake samun man fetur dinta a farashi mai rahusa.
Kamfanin Aliko Dangote ya bayyana cewa ana samun man fetur dinsa gidan man MRS da wasu gidajen mai a fadin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng