'Dan Majalisa Ya Fusata, Ya Nemi a Binciki Rushe Shagunan Talakawa 500 a Kano
- Majalisar Dokokin Kano ta karɓi ƙorafin ɗan majalisa mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad, kan rushewar shagunan ‘yan kasuwa a yankinsa
- Ɗan majalisar ya koka da cewa an jefa masu shagunan da abin ya shafa aa mawuyacin hali bayan an raba su da inda suke samun halaliyarsu
- A matakin da majalisar ta ɗauka, an kafa kwamiti domin binciken yadda aka rushe shagunan da kuma ka’idar da aka bi wajen aiwatar da haka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum bakwai domin binciken rushe shaguna sama da 500 a kasuwar Rano da ke karamar Hukumar Rano.
An ɗauki wannan mataki ne bayan dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad (NNPP-Rano) ya gabatar da ƙudirin gaggawa a zaman ranar Litinin.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ɗan majalisar ya bayyana rusau ɗin a matsayin abin takaici, yana mai kira ga majalisar da ta shiga tsakani,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci majalsisar da ta gaggauta gudanar da bincike domin gano dalilan da suka haddasa hakan.
Kano: Ɗan majalisa ya fusata da rushe shaguna
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Ibrahim Muhammad ya nemi a fayyace dalilin rushe shagunan, yana mai jaddada cewa lamarin ya jefa ‘yan kasuwa da dama cikin kunci.
Ya ce da yawa daga cikin 'yan kasuwar da abin ya shafa sun fada a cikin mawuyacin hali saboda sun rasa hanyoyin samun abincinsu.
'Dan majalisar ya kuma nemi sanin halaccin rushe shagunan domin 'yan kasuwar da abin ya shafa ba su samu isasshen gargadi ko diyya ba kafin a rushe musu wuraren kasuwanci ba.
Majalisar Kano ta ɗauki mataki kan rusau
Da yake mayar da martani ga ƙudirin, Shugaban Majalisar, Rt. Hon Isma'il Falgore, ya ba da umarnin kafa kwamitin mutum bakwai domin gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta

Asali: Facebook
Falgore ya bayyana cewa aikin kwamitin shi ne gano hakikanin dalilin da ya sa shugaban ƙaramar hukumar ya rusa shagunan.
Ya ce:
"Haka kuma za su binciki ko an bi ƙa’ida wajen aiwatar da wannan rusau, tare da bayar da shawarar matakan da ya dace a ɗauka domin hana irin wannan faruwa a nan gaba."
Majalisar dokoki za ta binciki rusau a Kano
A cewar Rt. Hon Isma'il Falgore, kwamitin zai kasance ƙarƙashin mataimakin shugaban Majalisar, Muhammad Bello Butu-Butu, kuma ana sa ran zai miƙa rahotonsa cikin mako guda.
Rahotanni sun bayyana cewa rushewar shagunan da aka yi makon da ya gabata ya haifar da zanga-zanga daga ‘yan kasuwa da mazauna yankin Rano.
Mutane da dama sun bukaci gwamnatin jihar ta biya diyya tare da samar da sabon wurin kasuwanci ga waɗanda abin ya shafa.
An fara ciyar da talakawa a Kano
A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da shirin ciyar da bayin Allah da ke azumin watan Ramadan akalla 91,000 a sassa daban-daban na jihar Kano.
Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya kaddamar da shirin ciyarwar a ranar Litinin, ya kuma ce an yi kyakkyawan shiri don komai ya tafi daidai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng