Mu Je Zuwa: Kamfanin NNPCL Ya Bi Sahun Dangote, Ya Rage Farashin Fetur a Kasuwa
- Ana ci gaba da gasa a tsakanin matatar mai ta Dangote da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) kan farashin fetur
- Kamfanin NNPCL ya bi sahun matatar Dangote wajen rage farashin da yake siyar da litar fetur a gidajen mai da ya mallaka
- A ranar Litinin, kamfanin na NNPCL ya rage farashin litar mai daga N945 zuwa a N860 a gidajen man da ke birnin Legas
- Duk da cewa kamfanin bai sanar da yin ragin a hukumance ba, ƴan kasuwar man fetur sun tabbatar da cewa an rage kuɗin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya bi sahun matatar Dangote wajen rage farashin fetur.
Hakan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta rage farashin fetur wanda shi ne na biyu a cikin wata ɗaya.

Asali: Twitter
NNPCL ya rage farashin litar fetur
Jaridar The Punch ta rahoto cewa wasu gidajen mai mallakar kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) sun sauya farashin litar fetur zuwa N860.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance daga kamfanin NNPCL, wasu gidajen mai a Legas sun rage farashin fetur zuwa N860 kan kowace lita.
An samu saukin ne daga N945 da ake sayarwa a ranar Lahadin da ta gabata.
Wannan na zuwa ne bayan da matatar mai ta Dangote ta rage farashin litar fetur daga N890 zuwa N825 a matakin sayarwa ga dillalai.
Kakakin kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, bai ɗauki kiran waya ko dawo da saƙonnin da aka tura masa dangane da wannan ci gaban ba.
Ƴan kasuwa sun tabbatar da ragin
Sai dai mataimakin shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), Hammed Fashola, ya tabbatar da rage farashin.
"Eh, gaskiya ne, NNPCL na sayar da fetur kan N860 a gidajen mai. Duk da cewa ba a saka wannan sauyin a shafin su ba tukuna, sun ce suna aiki don sabunta bayanan."
- Hammed Fashola
Haka zalika, shugaban ƙungiyar masu gidajen mai ta Najeriya (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya tabbatar da rage farashin kuɗin fetur da kamfanin NNPCL ya yi.
“Sun rage farashin fetur tun da safiyar yau, amma ban samu cikakken bayani ba tukuna."
- Billy Gillis-Harry
A ranar Laraba ta makon da ya gabata, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin fetur, wanda ya haifar da sabon tsarin farashi a kasuwar man fetur ta Najeriya.
Kamfanin NNPCL zai ƙara yawan gidajen mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) yana shirin ƙara adadin tashoshin mai da yake da su a faɗin ƙasar nan.
Kamfanin ya bayyana aniyarsa ta ƙara adadin daga 1000 zuwa 2000 kafin ƙarshen shekarar 2025 da muke ciki.
Ƙakakin kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa shirin faɗaɗa yawan tashoshin man, na da nufin sauƙaƙawa ƴan Najeriya wajen shan wahalar samun fetur.
Ƙarin tashoshin na man fetur zai taimaka wajen magance ƙarancinsa a wasu yankunan Najeriya da ke fama da matsalar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng