'Yan Ta'adda Sun Mamaye Wani Yanki na Abuja? 'Yan Sanda Sun Yi Bayani
- Wasu rahotanni sun yi yawo a kafafen sada zumunta masu iƙirarin cewa an sanya dokar hana fita a Abuja saboda ɓullar ƴan ta'adda
- Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fito ta ƙaryata waɗannan rahotannin inda ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikinsu
- A wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar, ya bayyana cewa ko kaɗan babu batun kasancewar ƴan ta'adda 79 a yankin Lugbe a Abuja
- Muyiwa Adejobi ya yi kira ga jama'a da su san irin labaran da za su riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya (NPF) ta yi magana kan rahotannin da ke cewa wasu ƴan ta'adda sun samu mafaka a babban birnin Abuja.
Rundunar ƴan sandan ta ƙaryata iƙirarin wanda ke yawo a kafafen sada zumunta mai cewa ƴan ta’adda 79 suna fakewa a Lugbe da wasu yankunan Abuja.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Lahadi a shafin X na dakarun.
Me ƴan sanda suka ce kan ƴan ta'adda a Abuja?
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa labarin wanda ke yawo a kafafen sada zumunta, ciki har da WhatsApp da ke bayyana kafa dokar hana fita a yankin Lugbe na Abuja, babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.
Olumuyiwa Adejobi ya ce bayanan sirri da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro suka tattara sun nuna cewa babu ƴan ta’adda da ke fakewa a yankin.
"Rundunar ƴan sanda ta ƙaryata wannan ikirari baki ɗaya. Bisa bayanan sirri da sashen leƙen asiri na ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro suka tattara, babu ƴan ta’adda da ke fakewa a yankin Lugbe na babban birnin tarayya Abuja."
"Rundunar ƴan sanda ta yi imani da cewa wani ko wasu da ke da mugun nufi ne suka ƙirkiri wannan saƙo da manufar haifar da firgici, tayar da hankalin jama’a, da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da ke gudana a Abuja."
"Rundunar ƴan sandan Najeriya na kira ga jama’a da su yi taka tsantsan wajen yaɗa bayanai a intanet, kuma su tabbatar da sahihancin duk wani gargaɗi da ya shafi tsaro daga hukumomin da suka dace kafin su watsa shi."
"Ya kamata ƴan kasa su yi watsi da duk wani labari ko bayani da ba daga ingantattun majiyoyin ƴan sanda ya fito ba, kuma ka da su firgita da labaran da ba a tabbatar da ingancinsu ba da ke yawo a kafafen sada zumunta."
- Olumuyiwa Adejobi
An yi wa ƴan san sanda tayin cin hanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu masu safarar yara sun yi wa jami'an ƴan sanda tayin cin hancin N1m a jihar Imo.
Jami'an ƴan sandan sun ƙi karɓar cin hancin, suka yi caraf da mutanen guda biyu waɗanda ake zargi da aikata mugun laifin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

