Dangote Ya Fadi Gidajen Man da za a Rika Samun Fetur Dinsa a Farashi Mai Rahusa

Dangote Ya Fadi Gidajen Man da za a Rika Samun Fetur Dinsa a Farashi Mai Rahusa

  • Bayan sauke farashi, matatar Dangote ta bayyana gidajen mai da ake sayar da man fetur dinta a dukkan jihohin a Najeriya
  • Matatar Dangote ta fitar da jerin farashin litar fetur a gidajen MRS, AP da Heyden a yankuna daban-daban na kasar nan
  • Biyo bayan haka, kamfanin na Aliko Dangote ya bukaci karin masu gidajen mai da su hada kai da shi domin amfanar jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan rage farashin man fetur da kamfanin Dangote ya yi, an bayyana jerin gidajen mai da ake sayar da shi a Najeriya.

Alhaji Aliko Dangote ya fitar da wannan sanarwa ne domin bai wa masu abubuwan hawa damar sanin inda za su samu fetur dinsa a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

Dangote ya ragewa 'yan kasuwa N16bn domin sauke farashin fetur a Najeriya

Dangote
Wuraren da ake samun fetur din Dangote. Hoto: Dangote Industries|MRS Oil and Gas
Asali: UGC

Legit ta tattaro bayanin da matatar Dangote ta yi ne a cikin wani sako da rukunin kamfanonin Dangote ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, Dangote ya bukaci sauran masu gidajen mai da su hada kai da shi domin al’umma su ci moriyar wannan rangwame.

Farashin fetur a gidajen man MRS

Kamfanin MRS na sayar da man fetur na Dangote a farashi kamar haka:

  • Legas: N860 duk lita
  • Kudu maso Yamma: N870 duk lita
  • Jihohin Arewa: N880 duk lita
  • Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas: N890 duk lita

Hakan na nufin cewa ‘yan Najeriya za su iya samun fetur din Dangote a farashi mai sauki a gidajen man MRS da ke fadin kasar nan.

Farashin fetur a gidajen man AP da Heyden

Baya ga gidajen MRS, gidajen mai AP da Heyden suma suna sayar da man fetur na Dangote. Ga jerin farashin su kamar haka:

Kara karanta wannan

Ramadan: Hukumar Hisbah ta ci gaba da aikin Allah cikin watan Azumi a Kano

  • Legas: N865 duk lita
  • Kudu maso Yamma: N875 duk lita
  • Jihohin Arewa: N885 duk lita
  • Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas: N895 duk lita

Wannan na nufin cewa akwai zabin gidajen mai daban-daban da masu abubuwan hawa za su iya samu domin sayen fetur din Dangote a fadin Najeriya.

Dangote ya bukaci karin hadin gwiwa

Kamfanin Dangote ya yi kira ga karin gidajen mai da su hada kai da shi domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci gajiyar wannan rangwame.

A cewar Aliko Dangote:

"Muna maraba da karin masu gidajen mai da za su hada kai da mu domin 'yan Najeriya su ci moriyar wannan tagomashi."
Mutane na sayen fetur
Mutane na sayen fetur. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Bayan haka, ‘yan Najeriya sun nuna godiyarsu ga Dangote bisa kokarinsa na rage farashin fetur domin saukaka wa mutane wahalhalun rayuwa.

Wasu daga cikin direbobi sun bayyana cewa wannan saukin farashi zai taimaka musu wajen rage kudin tafiya da kuma rage wahalhalu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kai farmaki zazzafa, sun kama 'yan fashi 35 masu tare hanyoyi

Dangote zai ragewa 'yan kasuwa N16bn

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta yi kira ga 'yan kasuwa da suke sayen fetur a wajenta da su dawo sayar da mai a sabon farashin matatar.

Matatar Dangote ta yi alkawarin cewa za ta mayar wa gidajen man kudin da ya karu bayan ta rage farashi a farkon watan azumi domin saukakawa talakawa a Ramadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng