'Yan Sanda, DSS Sun Mamaye Zauren Majalisa, Kakakin Majalisa Ta Shirya Yin Murabus

'Yan Sanda, DSS Sun Mamaye Zauren Majalisa, Kakakin Majalisa Ta Shirya Yin Murabus

  • Jami’an tsaro sun mamaye harabar majalisar dokokin Legas, inda suka hana ‘yan jarida shiga zaman da aka shirya yi ranar Litinin
  • Jibge jami'an tsaron ya biyo bayan dawowar Mudashiru Obasa, tsohon kakakin majalisar da aka tsige, wanda yaki yarda da tsigewar
  • Bayan wani taro da gwamnati ta gudanar, ana sa ran kakakin majalisar Legas ta yanzu, Mojisola Meranda za ta yi murabus a yau

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jami’an tsaro sun mamaye harabar majalisar dokokin jihar Legas, inda suka hana ‘yan jarida shiga zaman majalisar da aka shirya yi ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa za a fara zaman ne da misalin karfe 1:00 na rana, sai dai tsauraran matakan tsaro sun hana ‘yan jarida shiga.

Jami'an tsaro sun mamaye zauren majalisar Legas
An jibge jami'an tsaro a ciki da wajen zauren majalisar jihar Legas. Hoto: @LagosJunction
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun mamaye zauren majalisar Legas

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar Legas ta ji matsin lamba, ta yi murabus daga mukaminta

Jami’an tsaron sun hada da ‘yan sanda, jami’an tsaron farar hula, da kuma jami’an tsaro na jihar Legas, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin tsaurara tsaro ya biyo bayan dawowar tsigaggen kakakin majalisar jihar, Mudashiru Obasa, zuwa majalisar a ranar Alhamis.

Obasa ya jawo cece-kuce bayan dawowarsa, ya jaddada cewa har yanzu shi ne kakakin majalisar, duk da an tsige shi a ranar 13 ga Janairu, 2025.

Majalisar dokokin Legas mai ‘yan majalisa 40, ta tsige Obasa ne da kuri’un fiye da 'yan majalisa 30, sai daga bisani aka nada Mojisola Meranda a matsayin sabuwar kakaka.

Kakakin majalisar Legas ta shirya yin murabus

Ana sa ran kakakin majalisar Legas, Merinda za ta yi murabus daga mukaminta
Kakakin majalisar Legas, Merinda, ta shirya yin murabus daga mukaminta. Hoto: @lshaofficial
Asali: Twitter

Alamu na nuna cewa rikicin na gab da zuwa karshe, bayan da aka samu wani rahoton Daily Trust da ke nuna cewa Mojisola Meranda na shirin yin murabus daga mukaminta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

Murabus din Meranda za ta bude hanya ga dawowar Mudashiru Obasa, wanda majiyoyi suka ce shi ma yana shirin yin murabus a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan wata ganawa da aka yi a daren Lahadi a gidan Legas na Marina, wanda ya samu halartar 'yan Kwamitin GAC, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, da ‘yan majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa an cimma matsaya a wannan taro, kuma ana sa ran za a aiwatar da matsayar yayin zaman majalisar da aka shirya yi a ranar Litinin.

A cewar wata majiya daga taron, dukkan bangarorin sun bayyana ra’ayoyinsu, kuma an cimma matsaya da za ta kawo karshen rikicin da ya hana majalisar ci gaba da aiki.

An janye masu gadin kakakin majalisar Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an janye dukkan jami’an tsaron da ke kula da shugabar majalisar dokokin jihar Legas, Mojisola Meranda, wanda ke haifar da barazanar tsaro gare ta.

Kara karanta wannan

"Karya kake yi," Ƴan Majalisa 36 sun ƙara yi wa kakaki bore, sun tabbatar da tsige shi

Wani hadimi ga Rt. Hon. Mojisola Meranda ya tabbatar da cewa an janye dukkan jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda da jami’an DSS.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da magatakardar majalisar da aka tsige ke kokarin komawa ofishinsa, lamarin da ya haddasa hatsaniya a ranar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.